Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin jihar Gombe ta baiwa gwamnatin jihar Yobe tallafin Naira Miliyan Hamsin domin tallafawa kokarinta na tallafawa wadanda rikicin Mafa ya shafa, da ambaliyar ruwa a fadin jihar.
Mataimakin Gwamnan Jihar Gombe, Mista Manesiah Daniel Jatau, wanda ya wakilci Gwamna Inuwa Yahaya shi ne ya gabatar da wannan tallafi ga Gwamnna Buni a gidan gwamnatin Jihar da ke garin Damaturu.
Ya Kara bayyana cewar ,harin da aka kai wa al’umma da ta kai ga kashe wasu mutane da jikkata wasu a matsayin abin bakin ciki da ban takaici matukar gaske.
“Muna ba ku hakurin jure wannan rashi cikin harin da aka kai wa al’ummar da ba su ci ba na su Sha ba, da kuma ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyyar salwantar wasu gidaje da gonaki,” inji shi.
Don haka ne Gwamnan ya ce wannan tallafin naira miliyan 50 an yi ne domin tallafa wa gwamnatin jihar wajen tallafawa wadanda abin ya shafa.
Da ya ke mayar da jawabi, Gwamna Mai Mala Buni ya yabawa gwamnatin jihar Gombe bisa goyon bayan gwamnati da al’ummar jihar Yobe a irin wannan lokaci.
“Na yi matukar farin ciki da wannan nuna juyayi da ‘yan uwantaka da gwamnatin jihar Gombe ta nuna mana, za mu ci gaba da nuna goyon baya dangane da wannan kulawa kan wannan ziyarar da kuka kawo mana ta ‘yan uwantaka,” in ji Buni.
Ya ce kalubalen tsaro wani lamari ne da ya shafi duniya wanda ke bukatar hadin gwiwa don duba matsalar.