An tura karin sojoji a garin Moriki da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, yayin da wa’adin biyan harajin Naira miliyan 30 da Kasurgumin shugaban ‘yan bindigan nan, Bello Turji ya kakaba wa al’umma, ya cika.
Turji ya saka harajin Miliyan 30 a kan al’ummar yankin biyo bayan kashe masa shanu sama da 100 da sojoji suka yi masa kimanin makonni uku da suka gabata.
An rahoto cewa, sojoji sun harbe shanun ne a Dumfawa, wani kauye tsakanin Moriki da garin Shinkafi a cikin watan Agusta.
Da yake tabbatar da tura sojojin, wani mazaunin yankin, Aminu Musa, ya ce, an tura karin sojoji yankin a kwanakin baya.
“Baya ga sojoji, gwamnatin jihar ta kuma aike da karin jami’an tsaronta, na CPG zuwa yankin domin karawa jami’an kaimi.
“Mun yi farin cikin ganin jami’an tsaro a cikin yankunan mu. Shugaban rundunar ya ba mu tabbacin kare rayukan mu.”
Wani mazaunin garin, Iliyasu Ali, ya ce duk da karin jami’an tsaro da aka tura, akwai damuwa a tsakanin mazauna garin”.
“Akwai firgici da damuwa a tsakanin mazauna garin. Waɗannan ‘yan bindigar ba su da tausayi. Za su iya kai farmaki ga al’umma. Suna ɗauke da muggan makamai fiye da na sojoji. Don haka, jama’ar mu sun shiga cikin firgici matuka ganin cewa yau wa’adin biyan harajin ya kare.
“Allah ne kaɗai ya san abin da zai faru daga yau zuwa nan gaba. Tabbas ba mu biya harajin ba amma Turji ya yi alkawarin kawar da wannan al’umma idan har muka kasa biyan diyya ga shanunsa da aka kashe,” inji shi.
Leadership Hausa