Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin Yobe Ta Shawarci Al'ummomi A Kananan Hukumomi 9 Da Su Dauki...

Gwamnatin Yobe Ta Shawarci Al’ummomi A Kananan Hukumomi 9 Da Su Dauki Matakin Kariya Na Yiwuwar  Samun Ambaliyar Ruwa A Yankunan Su

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

A cigaba da samun iftila’in ambaliyar ruwa a yankuna da dama na Jihar Yobe, gwamnatin Jihar ta shawarci mazauna wasu al’ummomi a kananan hukumomi tara na jihar da su dauki matakan kariya sakamakon hasashen sake samun ambaliyar ruwa a yankunan su sakamakon sakin ruwa daga madatsun ruwa na Dadinkowa da Lagdo.

A cewar sanarwar kananan hukumomin sun hada da Bade, Nguru, Jakusko, Karasuwa, Yusufari, Geidam, Tarmuwa, Bursari, Machina, Fine da Gujba.

Wannan Gargadi gami da shawarar dai ta fito ne daga bakin Dokta Mohammed Goje, Babban Sakataren Hukumar ba da agajin gaggawa ba Jihar (SEMA)  a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu.

Ya kara da cewa sakin ruwa daga madatsun ruwa guda biyu zai kara jefa mazauna yankunan cikin mawuyacin hali, wadanda tuni ambaliyar ruwa ta shafa sakamakon mamakon ruwan da aka kwashe kwanaki ana yi.

“Jihar Yobe Jiha ce Dake Daya Daga ciki Jihohin kasar nan da ke  fuskantar ambaliyar ruwa tsakanin watan  15 ga Afrilu zuwa 9 ga Satumba 2024, wanda ya haifar da barna a kananan hukumomi da dama da ke jihar musamman ma a Kananan hukumomin da aka ambata da lamarin  yafi tsamari.

“A cewar babban sakataren na hukumar SEMA, wannan shawara ta kasance tamfar faɗakarwa don ƙarin ambaliya saboda yiwuwar fitowar ruwa daga dam ɗin Dadinkowa, Kogin Hadeja-Jama’are, Kogin Kamodugu, da kuma dam ɗin Lagdo a Kamaru,” in ji Goje.

Sakataren zartaswar ya shawarci mazauna yankunan da su dauki matakan kariya da suka hada da tafiya tudu domin ceton rayuka da dukiyoyin su.

“Ku kasance da masaniya ta hanyar sauraron bayanai akai-akai daga shugabannin gargajiya, kananan hukumomi da hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments