Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiZa Mu Gyara Hanyoyin Da Ambaliyar Ruwa Ta Barnata A Yobe, in...

Za Mu Gyara Hanyoyin Da Ambaliyar Ruwa Ta Barnata A Yobe, in ji Muhammad Alkali

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

A ziyarar duba wuraren da hanyoyin da hanyoyin da ambaliyar ruwan sama da ake shatatawa kamar da bakin kwarya a wasu yankunan Jihohin arewa maso gabas babban manajan daraktan hukumar raya arewa maso gabas (NEDC)  Alhaji Muhammad G. Alkali ya bayyana cewar, hukumar su na shirin daukar matakin bada tallafi da gyara hanyoyin da ambaliyar ruwa ta barnata a yankuna Jihar Yobe da ma sauran yankunan da suka hadu da irin wannan iftila’i na ambaliyar ruwa a Jihohin arewa maso gabas.

Manajan daraktan hukumar ta NEDC ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar gani da ido da ya kai a kananan hukumomin Nangere, Tarmuwa da Gujba don duba ambaliyar da ta lalata hanyoyin motar Potiskum zuwa Gashuwa, hanyar motar da ta tashi daga Damaturu zuwa Gashuwa , Geidam da kuma hanyar Damaturu zuwa Biu a Jihar Borno.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a yayin ziyarar babban Manajan hukumar ta NEDC ya bada tabbaci ga al’ummomin yankunan da wannan iftila’i ya shafa cewar, zai mika roko da koken al’ummomin yankunan ga gwamnatin tarayya kamar yadda suka nema  don ganin an yi wani abu akan lokaci lura da irin wahalhalun matsin rayuwa da ambaliyar ta jefa su  ciki.

Haka nan ita ma hukumar ta NEDC za ta yi namijin kokari don ganin ta kai daukin gaggawa ga al’ummomin da suka hadu da wannan iftila’i tare kuma da kokartawa don ganin an gyara wadannan hanyoyin mota.

Ya kuma  jajantawa al’ummomin da suka hadu da wannan iftila’i wadda a cewar sa wannan lamari su dauka lalle wata jarrabawa ne daga Allah SWT.

Babban Manajan ya kuma duba ayyukan gina ofishin hukumar da ke garin Damaturu da kuma wani babban dakin koyarwa da taruka da hukumar ta NEDC ta gina a Jami’ar Jihar Yobe cikin irin ayyukan da ta ke yi na tallafawa harkokin ilimi a yankunan na Arewa maso Gabas.

Wani daga cikin ‘yan Kungiyar direbobi ta kasa NURTW  a karamar hukumar Tarmuwa Malam Mustapha ya roki gwamnatin tarayya, gwamnatin Jihar Yobe da hukumar ta NEDC da su taimaka don ganin sun gyara musu hanyar su da ambaliyar ruwa ta yi awun gaba da ita lura da halin da matsin rayuwa  da wannan iftila’i ya jefa su ga shi kuma sun rasa gonaken su sama da 200.

Wannan ziyara dai ta samu rakiyar manyan jami’an hukumar da suka hada da babbarn jami’in hukumar na jIhar Yobe  Dr Ali Abbas da Sauran su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments