Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiYan Ta'addan Boko Haram Sun  Kashe, Sace Mana Mutanen Da Ba Mu...

Yan Ta’addan Boko Haram Sun  Kashe, Sace Mana Mutanen Da Ba Mu San Adadin Su Ba A Yobe..Wani Mazaunin Mafa

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Harin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai a garin Mafa da ke Karamar hukumar Tarmuwa cikin Jihar Yobe a yammacin ranar lahdi ya sa matukar juyayi ga al’ummar Jihar ta Yobe sakamakon irin kashe-kashen rayukan mutane masu tarin yawa da wadannan ‘yan ta’addan suka yi tare kuma da yin awun gaba da wasu matasa tarin yawa hade da kone kusan mafi yawa da illahirin gidajen garin.

Kan hakan ne Aminiya ta samu ganawa da wani mazaunin garin da ya sha da kyar  yadda ya samu isowa garin Damaturu amma ya ki amince wa da a nadi muryarsa  ko kuma daukar hoton sa, yadda aka saka ye sunan sa yadda ya tabbatar da wannan hari tare da karin haske da cewar, wadannan ‘yan ta’addan sun shigo garin su na Mafa ne da wajen karfe 4.30pm na la’asar kusan sun shigo da babura sama da 100 kuma kowane babur na dauke da mutane uku akan sa dauke da muggan makamai.

Daya daga cikin mazauna yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa, ‘yan ta’addan sun afkawa al’umma da makamai a kan babura kusan 100, inda suka kashe wasu da ba su ji ba ba su gani ba, tare da kona dukiyoyi ma su tarin yawa.

Wani mazaunin garin da ya kubuta daga harin, Malam Buba Adamu, ya kara da cewa wadanda harin ya rutsa da su akasarin su  kananan yara da matasa da kuma tsofaffi ne hade da mata, amma a halin yanzu, ba mu san takamaiman adadin mutanen da maharan suka kashe ba.”

A cewarsa, ‘yan ta’addar sun yi amfani da bindigogi da makaminkirar RPGs a lokacin harin a Mafa, tare da kona daukacin kauyen,” ya kara da cewa, “Babu wani abu da ya rage a kauyen kusan dukan illahirin kauyen yanzu toka ne ba kowa a kauyen yanzu, kusan kashi 80% na mutanen kauyen an kashe su har da kananan yara.”

Har ila yau, da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, wani shugaban al’ummar yankin, Lawan Mai Bano ya ce mayakan sun kai farmaki a garin na Mafa da yammacin ranar lahadi, inda ya tuna cewa tun makon da ya gabata ne mayakan Boko Haram suka yi barazanar kai hari kauyen amma ba su kawo ba sai a wannan karon.

Ya tabbatar da cewa an kashe mutane da dama, tare da kone sama da gidaje 1,000 baya ga shaguna, yayin da ‘yan ta’addan kuma suka yi awon gaba da abinci, suka kuma “kona komai a kauyen.”

Ya kara da cewa mayakan sun bude wuta ba kakkautawa tare da kashe mutane da dama yayin da wasu mazauna yankin suka tsere zuwa cikin daji.

“Babu wanda ya rage a ƙauyen kamar yadda nake magana da ku yanzu yayin da wasu mutane sun bace, an kashe su, wasu kuma sun gudu zuwa daji domin tsira.”

Don haka malamin ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su kara tura dakaru zuwa kauyen domin kare rayukan ‘yan kasa domin kaucewa sake afkuwar lamarin.

Bano ya kuma bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da matasa da dama, kafin su banka wa gidajen wuta.  “Ba mu san adadin mutanen da aka sace ba a yanzu.”

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce wani mazaunin garin Babagana Goni ya ruwaito cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai farmaki kauyen Mafa da yammacin ranar lahadi.

Abdulkarim ya kara da cewa maharan sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar lahadi, amma har yanzu ba a tantance adadin mutanen da maharan suka kashe ba.

Ya kara da cewa, “Ina so in sanar da ku cewa, a yanzu haka an tura jami’an mu da sojoji zuwa kauyen domin dawo da zaman lafiya bayan harin.  Muna aiki don samun cikakkun bayanai,” in ji Dungus.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments