Wani ma’aikacin filin jirgin sama, Auwal Ahmed Dankode ya mayar da dala 10,000 (Kimanin Naira miliyan 16) da aka samu a cikin wani jirgin sama ya yin da yake tsaftace shi a Kano.
Dankode, ma’aikacin Kamfanin Kula da Jiragen Sama na Najeriya (NAHCO) ne, a lokacin da yake tsaftace jirgin a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, sai ya ga kudin.
Da yake zantawa da manema labarai kan ci gaban, Auwal Ahmed Dankode ya ce ya gano kudin ne a wani jirgin saman kasar Masar da ya sauka da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba.
‘’Ina gudanar da aikin tsaftace jirgin da ya sauka ne sai na ga kudin a cikin ambulan.
Dankode da ya gano kudaden, ya ce a bisa horon da ya samu, duk lokacin da suka samu wani abu a cikin jirgin, ana sa ran su kai rahoto ga mai kula da su.
Duk da haka, ba a samun mai kula da shi ba a lokacin, don haka, nan da nan na kai rahoto ga manajan kamfanin jirgin don fara neman asalin mai kudin.
A cewarsa, bayan ‘yan mintoci, mai kudin, wani mutum ya garzaya zuwa cikin jirgin, domin neman kudin.
Ya lura cewa magidancin ya tambayi mutumin abin da yake nema, inda ya amsa da cewa kudi ne a cikin ambulan da ya manta a kujerar sa daya zauna, wato lambar kujerar da aka samu kudin.
‘’An yi wa mutumin tambayoyi da dama wadanda ya amsa da kyau kuma daga baya aka mayar masa da kudaden.
‘’Mutane da yawa a filin jirgin sun yaba mun bisa wannan aikin alheri dana yi.
”Gaskiya na ji dadi sosai da farin ciki da har na gagara in kwanta barci a yanzu, domin ina farin ciki da cewa Allah ya yi amfani da ni don faranta wa wani rai.”
‘’Mayar da abin da ba nawa ba ga mai shi ba komai ba ne a gare ni domin horon da muka samu daga gida kenan. Amma ina jin dadi da na san kimar kuma mai shi wanda bai jin Hausa da Larabci ya yi farin ciki har ya rungume ni sau da yawa.’’.
Auwal wanda dan asalin garin Kode ne a karamar hukumar Bunkure a jihar Kano, ya shahara da tsananin tsoron Allah da gaskiya.