Daga Rabiu Sanusi
Tsohon dan takarar majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Rogo a karkashin Jam’iyyar ADC Hon Haruna Yahaya Kadana ya bayyana cewa samun kwanciyar hankalin sa a yanzu bazai abinda bai wuce al’umma su samun shuwagabanni nagari ba.
Hon Kadana ya bayyana hakane a wata zantawa da manema labarai yayin da yake tsaka da murnar kara shekarun sa da yasamu aduniya da Allah ya azurta shi dasu da ya gudana a Cocin angilican dake karamar hukumar Fagge.
Matashin Dan siyasar ya kuma soki batun sayar da fom din takara akan naira milyan 10 na matakin zaben karamar hukuma, yayin da kuma ya bayyana shima ba Kansila bai kamata yakai naira milyan 5 ba.
“Wannan zai iya kawo koma baya ga nagartattun yan takara sukasa samun damar sayen wannan fom, kaga har yanzu daga su sai ‘Ya’Yan su kenan.
Kadana ya kuma bayyana wannan tsarin sayar da fom a matsayin ganin batun cin hanci da rashawa da ake bukatar dakilewa a matakin Qasa har zuwa kananan hukumomi a najeriya bazai taba gushewa ba.
Ya kuma bukaci cewa idan mulki mai girma Gwamna Abba Kabir daya sa baki domin a saukakama masu bukatar takara su samu sauqin sayen wannan takaradar takara dan yima al’umma aiki.
“anan ma muna kira ga Hukumar zabe ta jihar Kano da tayi dukkan mai yiwuwa wajen ganin wadanda suka kamata ne ta sayar ma da wannan fom tare da nemo hanyar da zasu samu saukin sayen wannan dom.
Hon Haruna Yahaya ya kuma cigaba da bayyana cewa babu yadda za’ai dan takara yasai fom da tsada amma ayi tunanin yayi ma jama’a aiki, wannan bakowa zai amince da hakan ba.
“A yanzu muna tunanin yadda al’umma zasu samu saukin rayuwa ne ba wai wani batun sauya sheka ko jam’iyya ba.
A yayin taron ne dai jama’a masoya daban-daban suka taya Hon Haruna Yahaya Kadana murna zagayowar haihuwar tashi tareda yi masa fatan alkhairi a dukka abinda yasa gaba,musamma yadda yake kulawa da al’umma tun daga matakin karamar hukumar shi ta Rogo har zuwa zagayen arewacin kasar nan dama wani yanki na Kudu.