Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga mambobin kungiyar likitoci ta kasa NARD da su janye yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da suka soma.
Karamin Ministan Lafiya Dakta Tunji Alausa ne ya yi wannan kira a ranar Alhamis a Kaduna a ziyarar da ya kai cibiyar kula da ido ta kasa.
A cewar Alausa, ana ci gaba da tattaunawa don tabbatar da an kuɓutar da abokiyar aikinsu da aka yi garkuwa da ita Dakta Ganiyat Popoola.
“Muna kan maganar, kuma mun tattauna da mai baiwa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu kan lamarin”, inji shi.
“Na kuma yi magana da kwamishinan ƴan Sanda kuma kowa yana bakin kokarinsa don ganin an sako ta,” ya ƙara.
Ministan ya ce a ranar Litinin din da ta gabata ya yi wata ganawa da shugabannin kungiyar ta NARD kan halin da ake ciki domin shawo kan su don janye yajin aikin domin hakan zai kara dagula lamarin harkokin lafiya.
Alausa ya ƙara da cewa masu garkuwa da mutanen sun ci gaba da canja bukatunsu a kowane lokaci, amma jami’an tsaro suna bakin kokarinsu don ganin an ceto ta cikin koshin lafiya.
Idan dai za a iya tunawa ‘ya’yan kungiyar sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai domin neman a ceto wata Likitan da ke Kaduna Dakta Ganiyat Popoola da aka garkuwa da ita.
An yi garkuwa da ma’aikaciyar likitancin a watan Disambar 2023, kuma yanzu ta shafe kusan watanni tara a wurin masu garkuwa da mutane.
A halin da ake ciki Shugaban ƙungiyar ta National Eye Center, Dakta Ibrahim Mohammed ya ce har yanzu yajin aikin na ci gaba da gudana.
Ya ce likitocin harkokin kiwon lafiya da na hakori ne suka shiga yajin aikin, kuma umarni ne daga hukumar ta ƙasa.