Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaBa Za Ka Iya Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Karkashin Pdp A...

Ba Za Ka Iya Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Karkashin Pdp A 2027 Ba – Bode George Ga Atiku

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Bode George, ya ce dole ne tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jira har shekarar 2031 idan har yana son sake tsayawa takarar shugaban kasa.

Ku tuna cewa Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya sha kaye a hannun shugaba mai ci Bola Tinubu.

George, a wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce dole ne dan kudu ya mamaye ofishin shugaban kasa da kuma kwamandan mulki daga shekarar 2023 zuwa 2031 “saboda wannan shine gaskiyar kasarmu, tsarin mulkin PDP da siyasarmu”.

“Ko a shekarar 2027, Atiku zai cika shekaru 81 kuma wannan ne lokacin da ya kamata ya rungumi ra’ayin shugaban kasar Amurka Joe Biden na bai wa matasa damar tsayawa takarar mukami mafi girma a kasar.

“Ba ni da wani abu na kaina game da Alhaji Abubakar. Abokina ne amma dole a fadi gaskiya. Nan da shekarar 2027, da yardar Allah, ni ma zan cika shekaru 80 a duniya.

“Don haka, me nake nema a ofishin gwamnati? Irin wannan ka’ida ya kamata ta shafi Alhaji Atiku Abubakar.

“Dukkanmu mun ga abin da Shugaban Amurka, Joe Biden, ya yi kwanan nan lokacin da ya sauka don Kamala Harris ta tsaya takarar shugaban kasa a watan Nuwamba.

“Wannan ita ce tambarin dan siyasa. Haka kuma ya kamata Alhaji Atiku Abubakar ya yi ta yadda a zaben shekarar 2027 PDP za ta tsayar da dan kudu a matsayin dan takarar shugaban kasa,” inji George, tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Ondo.

A cewarsa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan arewa daga jihar Katsina, ya bar mulki bayan shafe shekaru takwas yana mulki

Ya ce mulki a matakin tarayya ba zai iya zuwa Arewa a zaben shekarar 2027 ba saboda “hakikanin kasarmu da tsarin mulkin jam’iyyarmu ke nan”.

Jihon na PDP ya ce sashe na 7, karamin sashe na 3 (C) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ya bayyana cewa dole ne a kiyaye da tsarin shiyya-shiyya da karba-karba domin yin adalci da gaskiya a tsakanin al’umma.

Ya kara da cewa: “A jam’iyyarmu, wannan shi ne abin da ya dace kuma ya dace a yi a yanayin siyasar da muke ciki.

“Amma idan Alhaji Abubakar yana da burin sake tsayawa takara, zan ba shi shawara a matsayinsa na abokinsa, dan jam’iyya kuma dan uwa da ya jira har zuws shekarar 2031 da ke tafe. Zuwa lokacin zai cika shekaru 85 a duniya.

“A matsayinmu na ‘yan jam’iyya masu aminci, dole ne mu ci gaba da mutunta kundin tsarin mulkin PDP. Gaskiya ne. Na shiga jam’iyyar PDP a shekarar 1998 kuma na ci gaba da zama a wannan jam’iyyar tun daga lokacin ban gusa ba.”

Jigon na PDP ya ce an zabe shi mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa na (Kudu maso Yamma) sannan kuma ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a yanzu kuma memba na kwamitin amintattu (BoT) kuma daya daga cikin dattawan da ake mutuntawa da kuma sahihancin muryar jam’iyyar mu.

Ya ce: “Ban koma wata jam’iyya ba. Lokacin da nake Wadata Plaza, Atiku Abubakar yana cikin Villa a matsayin mataimakin shugaban kasa. Don haka mun san kanmu kuma mu biyu mun san ka’idojin da ke jagorantar wannan jam’iyya.

“Kada mu yi wani abu da zai ruguza jam’iyyarmu da kasa baki daya. A shekarar 2027, manufar ita ce jujjuya mulkin Najeriya dole ne jam’iyyar mu ta bi shi sosai.

“Don haka ‘yan Najeriya suna jiran mu kubutar da su a zaben shekarar 2027 amma dole ne dan kudu ya jagoranci yakin,” in ji shi.

George ya bayyana a matsayin abin dariya, wani rahoto da mai bai wa Abubakar shawara kan harkokin yada labarai, Mista Paul Ibe, ya fitar, inda ya kira shi (George) da mai nuna kabilanci, kan matsayinsa na karba-karba.

“Na karanta rahoton daya daga cikin masu taimaka wa Alhaji Abubakar kan harkokin yada labarai yana zargina da kabilanci, sai kawai na yi dariya. Babban abokina a yau shi ne Bafulatani Admiral Murtala Nyako.

“Ni ne Darakta-Janar na kungiyar yakin neman zaben Umaru Musa Yar’adua na zaben 2007. Marigayi shugaban ya aminta da ni. Don haka, ba za a zarge ni da nuna kabilanci ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments