Saturday, April 26, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiWadanda Ambaliyar Ruwa Ta Yiwa Barna Sun Samu Tallafin Kudi Daga Kungiyoyi...

Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Yiwa Barna Sun Samu Tallafin Kudi Daga Kungiyoyi Masu Zaman Kan Su A Yobe

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Akalla mutane 40 da bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su ne suka samu tallafin kudi daga wata kungiya mai zaman kanta ‘Gidauniya Agajin Gaggawa da Jinkai’.

Taron ya gudana ne a dakin taro na babban dakin taro na  CAMTECH Potiskum Multipurpose wadda  ya samu halartar wakilan sarakunan Fika da na Pataskum da sauran manyan malaman gargajiya da na addini.

Kafin raba kudaden ga mabukata da ambaliyar ruwa ta shafa, an  gudanar da taro inda aka tattauna hanyoyin da za a bi wajen aiwatar da dabarun taimaka wa magidanta yadda ya kamata.

A jawabinsa na bude taron,  Gidauniyar Agajin Gaggawa da Jinkai, Abubakar Mai Mai ya ce kungiyar ta damu da halin da al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa “musamman wadanda suka yi asara a gidajensu kasancewar gidaje da dama sun ruguje, abin da muka samu.

Don haka ne muka yi musu tayin agajin gaggawa ne kawai don ba su damar samun sauƙi a cikin zukatansu.

“Mun kuma Yaba da irin kokarin gwamnati a irin wadannan wuraren, amma muna ganin ya kamata mu ba da gudummawa a tsakaninmu da kuma taimaka wa jama’armu ba tare da la’akari da addini, siyasa, kabila, ko kowane irin ra’ayi ba.”

Mun gudanar da tarurruka da dama wadanda suka ba mu damar daukar bayanan al’ummar da abin ya shafa a fadin mazabu 10 na karamar hukumar Potiskum”.

Shugaban ya ci gaba da bayyana cewa shirin zai dore: “Za mu ci gaba da ba da gudumuwa don taimakawa marasa galihu;  yawancin mu masu rike da mukaman siyasa ne a gwamnatin jihar Yobe da kuma ‘yan kasuwa.  Karimcinmu ba wai kawai ya iyakance ga waɗanda ambaliyar ta shafa ba har ma da marasa lafiya marasa ƙarfi da aka kwantar da su a asibitoci suna buƙatar tallafi na gaggawa”.

A nasa bangaren, Sakataren kungiyar, wanda kuma shi ne Shettiman Malamai na Fika, Malam Abdulrazak, ya kawo wasu ayoyi daga Alkur’ani mai girma inda Allah ya bukaci bayinsa da su taimaka wa mabukata don ba su damar shiga Aljanna.

Da yake jawabi a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Malam Mohammed Nasir ya godewa kungiyar bisa gano matsalolin da suke fama da su tare da ba su tallafi “Mun ji matukar farin ciki da wannan kungiya ta damu da halin da muke ciki, wasun mu ba mu ci abinci ba kwana biyu da suka gabata wasu kuma suna barci da ido daya  saboda wani bangare na gidajenmu ya ruguje saboda tsananin ruwan sama, Muna godiya sosai kuma muna addu’ar Allah ya sakawa duk masu hannu da shuni da yawa da suka kawo musu wannan tallafi.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments