Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiJami'an Tsaro Sun Cafke Wani Mutum Da  Zargin Kokarin Fita  Da Injunan...

Jami’an Tsaro Sun Cafke Wani Mutum Da  Zargin Kokarin Fita  Da Injunan Shuka,  Famfon Ruwan Sha Da  Gwamnatin Yobe Ta Rarraba

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Dakarun rundunar ‘Forward Operations Base Potiskum’ a jihar Yobe sun cafke wani mutum mai shekaru 47, Malam Ahmed Abubakar bisa laifin kokarin fitar da wasu kayayyakin amfanin gona na jihar da aka raba wa manoma a kwanakin baya ya zuwa wasu Jihohin don sayarwa duk da dokar da gwamnatin Jihar ta yi na haramta hakan.

A wata sanarwa da mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (rtd) ya sanyawa hannu, ta ce sojojin sun kama wasu kayan aiki, tare da cafke wanda ake zargin a lokacin da ya ke dauke da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

A cewar Abdulsalam, wanda ake zargin na dauke ne da famfunan ruwa guda 5 da na’urorin hasken rana guda 8 da ake zargin na Daga cikin wasu kayayyaki ne da gwamnatin jihar Yobe ta raba domin karfafawa manoma a jihar.

Ya kuma bayyana cewa wanda ake zargin ya fito ne daga kauyen Dazigau da ke karamar hukumar Nangere kuma ya yi ikirarin cewa shi kansila ne mai wakiltar gundumar Dazigau a karamar hukumar, kuma kayan da aka samu a hannunsa na mutanen mazabarsa ne.

Janar Abdulsalam ya ci gaba da bayyana cewa wanda ake zargin bashi da takardun shine mai mallakar kayan ko wasu takardu da ke tabbatar da ikirarin sa a lokacin da aka kama shi.

Ya kara da cewa an mika wanda ake zargin ga hannun jami’an tsaron farar hula na (NSCDC) da ke Potiskum tare da kwato kayayyakin da ya ke dauke da su domin cigaba da daukar matakin da ya dace da shi.

A kwanakin baya ne dai Gwamnan Jihar Yobe ya rarraba kayayyakin noma ga Wasu manoman Jihar da suka fito daga dukannin mazabu Jihar 178 wadda shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu wadda Mataimakin sa Sanata Kashim Shettima ya wakilta, ya jagoranci rabawa a garin Damaturu a wani mataki na tabbatar da samar da abinci da kuma bunkasa wadatar abinci a jihar da kasa baki daya.

A cikin jawabin sa a wancan lokacin Gwamnan jihar, Mai Mala Buni ya roki jami’an tsaro da su kama duk wanda aka samu yana karkatar da kayayyakin amfanin gona a fadin kananan hukumomin 17 da ke Jihar.

Da yake zantawa da Aminiya a Damaturu, Kakakin Rundunar NSCDC na Jihar Yobe, Bala Garba ya tabbatar da kama wanda ake zargin.

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments