Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeIlimiKWALEJIN ILIMI TA ISA KAITA: JAGABA A WAJEN ILIMIN KOYARWA

KWALEJIN ILIMI TA ISA KAITA: JAGABA A WAJEN ILIMIN KOYARWA

Daga Sulaiman Usman Dutsinma

Babu ko tantama Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita da ke Dutsinma a cikin jihar Katsina ta ciri tuta a wajen Samar da ingantattu Kuma kwararrun dalibai da ke bayar da gudunmuwarsu a wajen habaka Ilimi a kowane mataki na jihar da Kuma wajenta.

Wani abin sha’awa da yabawa shi ne yadda hukumar makarantar da kokarin gwamnan jihar, Malam Umar Dikko Radda suka jajirce a wajen Samar da tsaro a waje da kewayen makarantar. Duk da barazanar tsaro da garin ke fuskanta amma dalibai da Malaman makarantar na zaune lafiya a cikin aminci ba tare da fuskatar wata barazana ba. Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) da Kuma kokarin hukumomin Kwalejin da Kuma goyon bayan gwamnatin Malam Dikko.

A bisa wannan aminci da aka samu ya Kara yawan daliban makarantar maza da mata. A ta bangaren Malaman kuwa yawan Malaman masu digiri na uku wato PhD ya karu.

Wani abin burgewa da sha’awa shi ne a yanzu haka hukumar kula da Kwalejojin Ilimi ta tantace tare da amincewa da dukkan kwasa-kwasa da Kwalejin ke gudanarwa.

An Kuma samu daidaito da hadin Kai a tsakanin masu ruwa da tsaki a wajen gudanar da al’amurran Kwalejin. Hadin kan ya hada da ma’aikatu da sassan gwamnatin da abin ya shafa.

Domin tabbatar da da ingancin aiki Kwalejin ta kafa Wani sashe na musamman da ke sanya ido a kan yadda al’ammurra ke gudanar a Kwalejin.

Dangane da ragowar dalibai masu son shiga Kwalejin kuwa wanna ya faru ne saboda ka’idojin hukumar JAMB wadda ta shafi jami’o’i da sauran makarantun. Wani lamarin Kuma shi ne yawan bude cibiyoyin karatu da jami’o’i ke yi a sassa daban daban.

Muna Kuma sane da lambar girma da wata makarantar firamare, Aya Primary School Funtua zata baiwa Kwalejin a a karshen wannan watan a bisa kokari da kwarewar da malamanta da suka halarci Kwalejin suke nunawa a wajen koyar da dalibai.

Kofa a bude take ga duk Wanda ke ganin ana aikata abin da ba daidai ba a Kwalejin da ya kawo rahoto ko ya Aiko takardar koke ga hukumomin Kwalejin.

Ya zama wajibi mu jinjinawa gwamna Malam Umar Dikko Radda, PhD da kwaminishinan ma’aikatar Ilimi mai zurfi da Kuma kanwa uwar gami shugaban Kwalejin Dr. Sama’ila Ado a bisa bunkasar da Kwalejin ke samu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments