Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), reshen jihar Yobe, Kwamared Rajab Isma’il Muhammed, ya bayyana damuwarsa da alhinin sa kan lalacewar wani bangaren na Sakatariyar Kungiyar da ke garin Damaturu sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a baya-bayan nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wani taron majalisar kungiyar da aka yi a sakatariyar kungiyar da ke Damaturu, yadda ya nuna irin barnar da ruwan sama ya yi a kewayen katanga da rufin Sakatariyar da sauran sassan ginin.
Rajab ya yi maraba da mambobin majalisar kuma ya yaba da sadaukarwar da suka yi na halartar taron duk da kalubalen tattalin arziki da ake ciki.
Ya jaddada mahimmancin biyan kuɗaɗen gudanar da harkokin Kungiyar tare da lura da cewa membobin da suke biya ne kawai za su iya cin gajiyar shirye-shiryen majalisar ta Jihar da kasa baki daya.
Shugaban ya sanar da cewa sakatariyar ta kasa ta ware wa jihar Yobe guraben wakilai 12 da mukamai biyar na masu sanya ido a jihar Yobe domin gudanar da taron wakilai na kasa da ke tafe, inda ya umurci kowane bangaren na shugabancin rassan Kungiyar da ya zabi mamba daya a matsayin wakilin da zai wakilce su.
Ya raba fom na tantancewa ga rassan Kungiyar (Chapels) inda ya umurci mambobin da su cike su kuma mika su cikin makonni biyu, yana mai gargadin cewa rashin yin hakan na iya haifar da asarar zama mamban kungiyar.
Shugaban ya jaddada muhimmancin kammala aikin tantancewa don kiyaye matsayin memba na kwarai ga Kungiyar.