Daga Rabiu Sanusi
An gudanar da bikin rantsar da malaman a sakatariyar karamar hukumar Ungogo, inda shugabannin al’umma, jami’an ilimi, da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.
A jawabinsa, Alhaji Sani Abdu Ungogo ya jaddada muhimmancin ingantaccen ilimi wajen ci gaban al’umma. Ya bayyana cewa sabbin malaman da aka rantsar za su taka muhimmiyar rawa wajen inganta ilimi a yankin, musamman a kauyuka da wuraren da ba su da wadatar Malaman .
Dan Majalisar Wakilai Mai wakiltar kananan hukumomin ungogo da munjibir Honarabul Sani Adamu Wakili, ya nuna godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda jajircewarsa wajen shirin BESDA da kuma himmarsa wajen inganta ilimi a karamar hukumar Ungogo.
Sani Adamu wakili Ya bukaci sabbin malaman da su goyi bayan shirye-shiryen ilimi a yankin ta hanyar aiki tukuru tare da hada kai da hukumomin makarantu na yankin domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ingantaccen ilimi.
Dayake jawabin sa Shugaban Dattawan jami’iyar NNPP na karamar hukumar kuma shugaban kwamitin ilimi Alh sammani Muhammad zango Shugaban ya yi alkawarin ci gaba da bai wa shirye-shiryen ilimi goyon bayan karamar hukuma. Ya kuma yi alkawarin samar da kayayyakin aiki da suka wajaba don samun nasarar shirin BESDA a Ungogo.
Yiya kira ga malaman da aka dauka na sa kai da su kasance masu himma a aikinsu tare da bada gudummawa mai kyau wajen bunkasa ilimi a al’umma.
Alhaji Sammani Muhammad Zango ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso saboda kokarinsu na shirya malamai da kuma karfafa su domin isar da ingantaccen ilimi ga dalibai. Ya jinjina wa Gwamnan bisa fifita jin dadin malamai da kuma fadada damar samun ilimi ga dukkan yara a jihar.
Malaman da suka rabauta da takardar kama aikin sun bayyana godiyarsu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda goyon bayansa ga sashen ilimi da kuma jajircewarsa wajen tabbatar da cewa kowane yaro a jihar ya samu ingantaccen ilimi.