Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeTsaroƳan bindiga sun kashe jami’in tsaro, suka yi garkuwa da iyalansa da...

Ƴan bindiga sun kashe jami’in tsaro, suka yi garkuwa da iyalansa da na makwabta a Magamar-Jibia dake jihar Katsina

… lamarin ya haifar da fargaba da zaman ɗar-ɗar a tsakanin mazauna yankin, inda suka yi kira ga hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa domin magance matsalar rashin tsaro da ke ƙara ƙamari a yankin.

Wani mummunan lamari ya faru a garin Magamar-Jibia da ke lardin Mazanya dake ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda wasu ƴan ta’adda suka kai hari gidan wani jami’in tsaro na kungiyar mafarauta ta Najeriya (HAN) Aliyu Yahaya, mai kimanin shekaru 31 da haihuwa.

Maharan sun bindige Aliyu ba tare da jin ƙai ba, wanda ya yi sanadin mutuwarsa, inda suka yi awon gaba da matarsa, ɗansa, da wasu mutane uku dake makwabta da shi.

Wani ɗan uwa ga marigayin, Salisu Yahaya, wanda ya ba jaridar Hausa Abcnews labarin abin da ya faru ya ce, “a ranar Talata, 13 ga watan Agusta, 2024, da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ƴan ta’adda ɗauke da makamai suka haura katangar gidan Aliyu, inda suka harbe shi da bindiga har lahira tare da ƙona gawarsa a cikin ɗakinsa.

‘Yan uwan ​​waɗanda abin ya shafa dai sun kasance cikin ruɗani da bakin ciki yayin da ‘yan bindigar ke aiwatar da harin nasu na rashin tausayi.

“Duk da cewa ɓatagarin sun kashe Aliyu, jinin ƴan bindigar da ya kwarara a ƙasa ya nuna jajircewarsa sosai wajen kare kansa da iyalansa daga harin ƴan ta’addan a cikin gidan.

Wani abokin aikin jami’in tsaron da ya mutu, Basiru Muhammad, ya koka kan mutuwar wannan matashi mai kishin ƙasa da ya rasa rai a fage daga yayin da yake tsaka da yiwa al’umma hidima, yana mai jaddada buƙatar a ƙara ɗaukar matakan tsaro domin daƙile afkuwar irin haka.

Mazauna yankin sun ta yin kiraye-kirayen ɗaukar mataki tare da yin tsokaci da nuna buƙatar masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da su yi duk mai yiyuwa domin nuna jin jin ƙai ka mamacin, inda suka buƙaci gwamnati ta shiga tsakani domin yaƙar barazanar ta’addanci da ke ƙara ƙamari a yankin.

Wani mutum da aka yi garkuwa da matansa biyu da surikarsa ɗaya, Amadu Bello, ya roƙi hukumomi da su ba da fifiko wajen ceto ƴan uwansu da aka yi garkuwa da su tare da kare al’umma daga fuskantar irin wannan ta’asar.

Shi kuwa Alhaji Sani Salisu, ya bayyana irin raunin da yankin ke fama da shi sakamakon rashin isassun jami’an tsaro, inda ya ƙara da cewa akwai bukatar a ɗauki matakan gaggawa domin kare mazauna yankin daga hare-haren ta’addanci.

“Mutane sun bayyana rashin zuwan jami’an tsaro da wuri domin fatattakar ƴan ta’addan a kan lokaci a matsayin abin da yake taimakawa wajen kai harin ta’addancin wanda ke cin rayukan mutane a ciki har da Aliyu da ɓatagarin suka kashe a baya-bayan nan; kuma hakan na ƙara jefa tsoro a cikin zukatan al’ummar yankin,” in ji shi.

Da yake bayyana damuwarsa kan matsalar rashin tsaro da ake fama da ita, Alhaji Aminu Dan Mugyanbo ya jaddada buƙatar ƙwararan matakai da Gwamna Dikko Umar Radda zai ɗauka domin magance matsalolin rashin tsaron da ke addabar Magamar-Jibia da sauran yankunan ƙaramar hukumar Jibia.

 

“Kasancewar garin na fuskantar ayyukan ta’addanci, hakan ya haifar da yanayi na fargaba da zaman ɗar-ɗar, wanda ya sanya muke ganin dole a ɗauki matakai cikin gaggawa domin dawo da zaman lafiya da tsaro,” in ji shi.

Yayin da al’umma ke kokawa kan wannan mummunan lamari, juriya da haɗin kan ƴaƴan kungiyar sa kai dake rajin tsaron rayuka da al’umma, na zama abin fatan alheri a gare su.

Tunawa da Aliyu Yahaya da waɗanda harin ya rutsa da su zai dawwama a matsayin tunatarwa kan yadda ake ci gaba da yaki da ta’addanci da kuma ƙudirin hadin gwiwa na shawo kan ƙalubalen rashin tsaro da ke barazana ga rayuwa da dukiyoyin al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments