Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa tashar jiragen ruwa ta kan Tudu za ta fara aiki a Birnin Maiduguri nan da watanni shida ma su zuwa.
Zulum ya bayyana hakan ne a Legas yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ziyarar ban girma da ya kai wa babban sakataren hukumar kula da jiragen ruwa ta Najeriya, Pius Akutah.
Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa kafa hukumar NSC, tare da samar da guraben ayyukan yi ga matasa, shi ma zai bunkasa tattalin arzikin jihar.
Ya ce: “Kafa tashar ruwan ta kan tudu a Maiduguri zai kawo damammaki da dama ga gwamnati da mutanen jihar Borno kwata tare da samar da aikin yi, kuma zai rage yawan gararamba da dubban yara kanana ke Yi kan titi wadda hakan na da matukar muhimmanci.
“Jihar Borno tana kan iyaka da kasashe uku, wato Nijar, Chadi da Kamaru wadda tashar jiragen ruwa ta cikin gida zai inganta kasuwancin kan iyaka.
Wannan shi ne abin da muke nema yadda dangantakar da ke tsakanin kasashen mu na kan iyaka za ta inganta, tattalin arzikin kasa ta yadda zai bunkasa sosai, kuma GDP namu zai karu.
“Muna kokarin kawar da hankalinmu daga bin hanyar tattalin arzikin daya-daya, wato mai, ta hanyar saka hannun jari a wasu damammaki, Ina ganin Najeriya za ta yi kyau nan ba da jimawa ba.”
Gwamnan ya bayyana cewa, “Gwamnatin tarayya na kokarin ganin an gyara layukan dogo a karkashin shirin shugaban kasa Bola Tinubu na habaka tattalin arzikin kasa.”
A cewar sa a halin da ake ciki gwamnatin tarayya na cikin aikin gyara dukkan hanyoyin, kuma dubban manyan motoci na shiga Maiduguri kullum.”
“A cewar sa Ko da babu layin dogo, tsarin sufurin hanya ba su da kyau a yanzu ga tashar ruwa ta kan tudu wadda zata taimaka matuka a cikin ƙasa, Muna sa ran za a shirya aikin nan da watanni shida.”
A nasa bangaren, babban sakataren hukumar ta NSC, Pius Akutah ya bayyana cewa, idan aka kafa tashar jirgin ruwa ta kan tudu a Maiduguri, za ta bunkasa harkokin cinikayyar kan iyaka, duba da cewa Borno na makwabtaka da kasashe uku na Kamaru, Chadi da Jamhuriyar Nijar.