Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLafiyaKungiyar Likitoci Ta Kasa  (NARD)Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Sa Baki...

Kungiyar Likitoci Ta Kasa  (NARD)Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Sa Baki Don Sako Mambar Kungiyar Da ‘Masu Garkuwa Suka Kama

Daga, Sani Gazas Chinade,
Azare

Kungiyar Likitoci ta kasa (NARD) reshen Cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya (FMC) da ke Azare ta bukaci gwamnatin tarayya da sa baki don sako daya daga cikin mamban kungiyar su da masu garkuwa da Mutane suka kame yau kusan kimanin watanni bakwai da ‘yan kwanaki.

Kungiyar ta likitoci ta bayyana hakan ne a wata zanga-zangar lumana da suka shirya suka kuma aiwatar a harabar cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya (FMC) da ke garin Azare cikin Jihar Bauchi dangane  wannan batu na kama mambar kungiyar ta su Dokta Ganiyat Popoola da ke aiki a babban asibitin ido na gwamnatin tarayya da ke Kaduna a watanni kimanin bakwai da ‘yan kwanaki wacce har yanzu tana hannun su.

A jawabinsa yayin da likitocin suka kai masa ziyara a ofishinsa babban Darakta a bangaren mulki na cibiyar kiwon lafiyar Muhammad Ibrahim kari
bada tabbaci yayi ga mambobin wannan kungiya kan cewar, za su yi wani namijin kokari don yin wani abu akai musamman ta wajen mika koken su ga hukumomin da suka dace don samo bakin zaren yadda za’a ceto wannan baiwar Allah kana ya kuma jajantawa mambobin wannan kungiya kan hakan.

Shi kuwa shugaban wannan Kungiya ta likitoci reshen cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya (FMC) reshen wannan cibiyar Dr. Ejembi Samuel A dakole a jawabin sa da farko yabawa yayi ga mambobin wannan kungiya dangane da goyon bayan da suka nuna na shiga wannan zanga-zanga ta lumana don tausayawa abokiyar aikin su Dr Ganiyat Popoola  da masu Garkuwa da mutane suka dace kusan Watanni bakwai da suka shude kana ya kuma nuna rashin Jin dadin su kan wannan lamari.

Shugaban Kungiyar ya kuma nuna bukatar da ke da akwai na gwamnatin tarayya da ta yi wani yunkurin don ceto rayuwar wannan baiwar Allah Dr Ganiyat Popoola wacce aka dauke ta da mijinta da wani Wanda ya zo wajen ta Hutu wadda daga bisani aka Sako mijin na ta bayan an basu kudin fansa kimanin Naira Miliyan 60 a cikin Naira Miliyan 100 da suka nema duk da cewar Sauran Naira Miliyan 40 da ya rage daga bisani an kai musu amma suka ki sake ta.

“A cewar shugaban a labarin da suka samu a halin yanzu wannan likita tana cikin wani mummunan hali na jinya tunda barin jikin ta daya ma ya samu matsala kana Sau guda ake bata abinci a cikin kwanaki uku.”

“Don haka ne suke rokon gwamnatin tarayya da dukkannin ma su ruwa da tsaki da ke kasar nan da su yi hobbasan don ganin an Sako Dr Ganiyat domin matuka akan gaza yin wani abu akai to kuwa su likitocin kasar nan ba su da wani zabi illa janye ayyukan su daga asibitocin kasar nan domin rayuwar su na cikin hadari matuka kasancewar a kasa da mako guda ma an sake garkuwa da wani mamban wannan kungiya da ke aiki a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Jos (JUTH) cikin Jihar Filato.”

Shi ma Sakataren wannan kungiya ta likitoci reshen FMC Azare Dr Umar faruwar a cikin jawabinsa cewa yayi su mambobin wannan kungiya suna cikin halin garari domin kuwa matukar gwamnati ba ta sa baki an sako wannan mamba ta su ba to kuwa rayuwar su na cikin kunci wadda ba su da wani zabi illa daukar matakin janyewa daga asibitocin kasar nan har sai an samu biyan bukata.

Ita kuwa Dr Rahama Ahmadu mambar kungiyar a cibiyar kiwon lafiyar cewa ta yi, su mata likitoci Kai tsaye wannan lamari ya taba su wadda alal hakika akwai bukatar daukar matakin gaggawa don ceto wannan abokiyar aiki na su kasancewar rayuwar ta na cikin mawuyacin halin da ta ke bukatar taimakon gaggawa don ceto rayuwar ta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments