Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaTarin magauta bai hana Gwamna Abba aiki ba--Hon Ibrahim Namadi

Tarin magauta bai hana Gwamna Abba aiki ba–Hon Ibrahim Namadi

Daga Rabiu Sanusi

Kwamishinan bibiyar ayukan gwamnatin jihar Kano Hon Ibrahim Namadi Dala ya bayyana cewa duk da tarin magauta da ke da kudurin maida jihar Kano baya,bai hana mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf gudanar da ayukan cigaba ba.

Hon Ibrahim Namadi Dala ya bayyana hakane ga manema labarai yayin zantawar sa da su a ofishin shi.

Kwamishinan ya tabbatar da ayukan alkhairi da gwamnan na Kano yake gudanar wa tare da taimakon mukarrabansa da yabasu amana da ya hadar da shi dake aiki a wannan ma’aikata mai amfani.

Namadi Dala yace wannan yasa basuyi kasa a gwuiwa ba wajen cigaba da bibiyar wadannan ayuka na mai girma gwamna bayan kama ragamar ayukan su a matsayin shugaban a wannan hukuma ta bibiyar ayukan gwamnati.

“A wannan aiki da mukeyi muna tabbatar da cewa dukkan ayukan da ba’a karasa ba tun lokacin tsohon gwamna sanata Rabiu Musa Kwankwaso.”

Haka zalika yakara da cewa wannan ayukan ne da gwamnatin data gabata bata kammala ba saboda rashin kishin jihar yasa ayanzu injiniya Abba Kabir ya ke karasawa dan amfanin al’umma.

Batun rashin komawar yan kwangila kuwa da aka samu tsaikon komawar su bakin aiki, Namadi Dala yace yana da alaka da yadda aka basu aiki a lokacin baya irin saukin kaya sai abinda yake na canjin farashin kayan aiki a halin yanzu.

“Amma kuma yanzu haka dukkan Yan kwangilar sun koma bakin aiki bayan zama da mai girma gwamna yayi dasu tare da basu dukkana abinda yakamata da hadin kai dan asamu damar karasa wannan ayuka a fadin kananan Hukumomin da muke dasu 44.

Sai dai Kwamishinan ya bukaci al’umma dasu kara taimakawa wajen addu’o’in da zasu kawo zaman lafiya ga wannan jiha kuma su taimakawa gwamnatin nan dan samun nasara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments