Daga Rabiu Sanusi
An bukaci jami’an Yansandan da suka samu karin Girma da su kara jajircewa wajen kamanta gaskiya da rikon amana yayin gudanar da aikin su.
Kiran na zuwa ne daga bakin kwamishinan Yan sandan Jihar Kano CP Solomon Garba Dogo yayin da yake dorama Jami’an Yansanda kimanin su 181 karin girma a ranar Litinin.
CP Solomon Garba Dogo yace kasancewar kwarewa kadai bazata ba jami’i damar zama a matakin gaba ba kadai har sai yayi wani kokari na ganin ya tsare aikin sa kamar yadda yakamata.
“Samun dan sanda da bayanai masu nagarta da kwarew yake sawa ya samu karin girma a dukkan aikin da yake yi.
Dogo wanda ake yiwa lakabi da (Dogon aiki) ya kuma godewa Babban sifeton Yan sanda na kasa Mr Kayode Adeolu da saura manyan mataimakan sa wajen yin dukkan mai yuwuwa ganin an samu nasara a wannan hukuma.
Kwamishinan Yan sandan ya kuma yaba da irin kokarin Jami’an bisa jajircewar su wajen kwantar da tarzoma da kare rayukan al’umma da dukiyoyin su, musamman lokacin zanga-zangar da ta gabata.
Da yake jawabi amadadin wadanda suka samu karin girman ASP Jacob Yadume , ya bada tabbacin zasu cigaba da aiki tukuru cikin kwarewar horarwar da suka samu kamar yadda dokar aikin ta tanadar.