Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabarai'Yan Kasuwa A Funtua Sun Roki Gwamna Radda Da A Jinkirta Rushe...

‘Yan Kasuwa A Funtua Sun Roki Gwamna Radda Da A Jinkirta Rushe Kasuwar 

Yan kasuwar sun yi wannan Kiran ne alokacin da suke zantawa da wakilin mu Saadu muntari saulawa a kasuwar dake funtua.

Sun bayyana cewa sakema kasuwar fasali da daga darajarta abune Mai kyau da ci gaba amma lokacin da aka ce za a gudanar da aikin ne bai dace da yanayin da yankasuwar suke ciki ba.

A ta bakin wadansu daga cikin Yan kasuwar irin su Alh Bature Mai wake da p R o kunkingiyar yan Hatsi shehu Dahiru maidawa sun bayyana cewa a halin yanzu Yan kasuwar suna fuskantar matsi na tattalin arziki da tabarbarewar harkokin kasuwanci saboda yanayin da tattalin arzikin kasa yake ciki.

Rushe kasuwar a halin yanzu da kuma to yankasuwar zai janyo asara, karewar arziki da na kasuwanci ga wasu dayawa a kasuwar musamman ma marasa karfi daga cikinsu.

Alh Kabir kasimu da Abubakar labaran na Yan Nika da Isah Na sumaila Mai maganin gargajiya sun bayyana cewa idan aka roshe kasuwar a halin yanzu za a jefa mafi yawancin Yan kasuwar a cikin tashin hankali tunda wasu bashi yayi madu yawa, kana ga karancin jari saboda tsadar kayayyaki.

Sun bayyana cewa a dan jinkirta aikin kasuwar zuwa nan gaba idan abubuwa suka daidaita sai Gwamnati tazo ta ci gaba da aiki.

Haka Sauran Yan kasuwar da aka zanta dasu Alh murtala Mai kabeji, Mrs Easter Odayabuci, Saadu zubairu da Danbaballe Mai chemist sun ce ya kamata Gwamnati tayi la,’akari da yanayin da aka keto na cutar Corona, da canjin kudi da dauke tallafin Mai da hauhawan farashin kaya Wanda yasa Yan kasuwa cikin damuwa na rashin jari.

Asaboda haka su kai kira ga Gwamna Dikko umar Radda da a bari yan kasuwat su farfado su biya basussukan da ake binsu kamin a roshe kasuwar.

Sun bada shawarar cewa ya kamata Gwamnati ta dibi wani waje a bayan garin funtua a Gina wata kasuwar sabuwa kamin a roshe wannan.

Hakan zai bada dama asake ma Yan kasuwar wuri ba tare da an taba kasuwan cin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments