Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin Jihar Katsina Ta Cire Dokar Takaita Zirga-Zairga Kwata-Kwata

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Cire Dokar Takaita Zirga-Zairga Kwata-Kwata

Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da cire dokar takaita zirga-zirga kwata-kwata wadda ta fara daga 10:00 na dare zuwa 4:00 na asuba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha Abdullahi Aliyu Yar’adua, kuma Accuracy News Hausa ta samu.

A cewar takardar, hakan na da nufin bada dama ga al’umma su cigaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum a cikin natsuwa.

Takardar ta kuma nuna godiyar Gwamnatin Jiha akan goyon baya da aka baiwa Gwamnatin na bin dokar da aka sanya wadda take da nufin tabbatar da zaman lafiya a Jihar nan.

Ta kuma shawarci jama’a akan kada su yi kasa a guiwa wurin cigaba da yin addu’oin wanzuwar zaman lafiya da karuwar arziki a Jihar Katsina da Kasa baki Daya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments