“Alal hakikanin gaskiya na yi niyyar yin wannan rubutu ne saboda wasu yan abubuwa da ke faruwa a cikin aikin Jarida na wannan zamani da za’a iya dangantawa da matsalolin da ke tasowa a cikin aikin a wannan zamani”.
“Kamar yadda yake a ilimance, duk wanda ya san wanene ake kira Dan Jarida, to ya san cewa shine wanda ya karanta karamar Diploma ta Kasa, ko kuma makamancin ta wato, professional Diploma in Journalism”.
“Wadannan sune abinda ya kamata mutane su fahimta, kamar yadda manazarta ilimi suka yadda da shi akan cewa duk wanda ya yi wadannan karatuttukan biyu shine za’a kira da Dan Jarida”.
“Babbar matsalar a nan ita ce, mafi yawancin mutane sun kasa su fahimci hakan, lura da yadda suke mu’amala da wasu mutane da suke aiki da su a matsayin Yan Jarida”.
“Yana da kyau a gane cewa akwai Dan Jarida akwai kuma Ma’aikacin Jarida wanda banbancin su a bayyane yake”.
“Kamar yadda na ambata a baya, shi Dan Jarida mutum ne wanda ya yi wancan karatun da na ambata a baya, wanda a karatun nashi ya san dokoki da sharudda na aikin”.
“Shi kuma Ma’aikacin Jarida mutum ne wanda yake aikin Jarida amma bai yi karatun aikin ba, sai dai yana aiwatar da shi a aikace”.
“To wadannan abubuwa guda biyu su ne ya kamata mutane su fahimta a duk lokacin da zasu yi mu’amala ta aikin jarida da wani mutum”.
“A halin yanzu abubuwa da yawa na tasowa a cikin aikin na jarida, wanda zaka ga wasu ma’aikatan jaridar suna aikata ba dai-dai ba”.
“To a nan wurin yana da kyau a yi wa Malam Dan Jarida adalci ta hanyar gano shin irin wadancan mutane da ke aikata abinda suka ga dama shin sun karanta aikin na jarida Koko akasin hakan?”.
“Saboda haka abin a bayyane yake dai akwai Dan Jarida akwai ma’aikacin Jarida”.