Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiDangane Da Cin Gashin Kai Na Kananan Hukumomin Najeriya

Dangane Da Cin Gashin Kai Na Kananan Hukumomin Najeriya

Shin Ko Kun San Cewa Kowace Karamar Hukuma Za Ta Iya Daukar Ma’aikata Dubu 1,200 Aiki Kuma Ta Dinga Biyansu Albashin Naira Dubu 200 A Duk Wata?

Kowace ƙaramar hukuma a Nijeriya tana da karfin daukar ma’aikata dubu 1,200 ta riƙa biyansu albashin naira dubu 200 a matsayin mafi ƙarancin albashi a duk wata.

Alƙalumman kudaɗen da Gwamnatin tarayya ta turawa ƙananan hukumomi kai tsaye a asusun su na watan Agusta ne ya nuna haka:

Karanta:

Kananan Hukumomi a Kudu Maso Yamma sun sami Naira Biliyan N63,950,000,000.00 na ƙananan hukumomi 137.

Aƙalla kowace ƙaramar hukuma za ta sami kimanin Naira milyan 460,000,000.00.

Idan tana da ma’aikata 1,200 ace za ta biya kowannensu Naira dubu N200,000 a wata zai kama Naira N240,000,000.

Kenan shugaban ƙaramar hukuma yana da ragowar rarar fiye da Naira milyan N200 kuma fa wannan banda kudin da ƙaramar hukumar za ta samu na kudaden shigar ta da na haraji.

Sai Ƙananan hukumomin yankin Arewa maso Yamma sun samu Naira Biliyan N62,780,000,000.00 na ƙananan hukumomi 186

Sai Ƙananan hukumomin shiyyar Kudu maso kudu sun sami Naira Biliyan N44,520,000,000.00 na ƙananan hukumomi 123.

Shiyyar Arewa ta tsakiya sun sami naira Biliyan N38,110,000,000.00 na ƙananan hukumomi 115.

Sai Shiyyar Arewa maso Gabas sun tashi da Naira Biliyan N37,870,000,000.00 na ƙananan hukumomi 112

Shiyyar Kudu maso Gabas sun sami naira biliyan N30,620,000,000.00 na ƙananan hukumomi 95.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments