Daga Rabiu Sanusi
Shugaban Jam’iyyar SDP na jihar Kano kuma sakataren Gamayyar hadakar Jam’iyyu Hon Ali Shettima Tudun Murtala ya bayyana cewa shirye-shiryen Jam’iyyar su yayi nisa wajen batun tunkarar Zaben Kananan Hukumomi da za’a gudanar a jihar Kano.
Hon Ali Tudun Murtala ya bayyana haka ne a wata zantawa da Wakilan Jaridu da yayi adai dai lokacin da yakema wakilan Gidajen Jaridu Karin Haske ka. Shirin Jam’iyyar SDP.
Shugaban Jam’iyyar SDPn yace a yanayin da ake ciki yanzu yana da tabbacin Jama’a ne zasu zama alkalai bisa irin yadda al’umma suke cikin halin matsin Rayuwa.
Hon Ali wanda kuma shine sakataren tsare-tsaren gamayyar Jam’iyyu a jihar Kano yace ba karamin alkhairi bane gare su bisa bada umarnin gudanar da Zaben Kananan Hukumomi a fadin Kasar nan.
“Bamu da abinda zamu iya cewa a halin yanzu da ya wuce shugaban Hukumar zabe na jihar Kano yayi adalci lokacin gudanar da wannan zabe.
Shugaban na SDP ya kuma ce idan shugaban zabe Prof Malumfashi ya tsaya yayi nazari zai ga babu abinda al’umma suke bukata da ya wuce shugaban da suka zaba ba abinda wani bangare yake bukata.
“Batun shiri na tunkarar zabe muna nan muna shiri,dan haka bazamu ba abokan hamayya satar amsa ba(DARIYA) amma muna shiri kuma akwai nasara in sha Allahu.”
“Mun san Shi Baturen zabe na wannan. Jihar tamu mutum ne wanda yasan abinda yake yi dan haka bamu da matsala kamar yadda mukayi magana da shi a wani taron shugabannin Jam’iyyu da muka yi kasa da kwana biyu ya bayyana mana kudurin sa na gudabar da sahihin zabe, muna da kyakkyawar fahimta tare da sa ran zai kamanta adalci.