Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da sassauta dokar takaita zirga-zirga da ta sanya biyo bayan zanga-zangar game gari da aka gudanar a fadin Najeriya.
Mukkadashin Gwamnan Jihar Malam Faruq Lawal, ne ya amince da sassauta dokar, domin baiwa jama’a sukunin cigaba da harkokin su.
Kamar yadda Accuracy News Hausa ta samu, an takaita zirga-zirgar ne daga bakwai na dare zuwa karfe 10 na dare a cikin Garin Katsina da kewaye.