‘Yan bindiga sun sace matar wakilin jaridar New Telegraph a Jihar Kogi, Muhammed Bashir, tare da ‘ya’yansu mata guda biyu. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Kaduna, inda matar Bashir da ‘ya’yansu suka je yin hutu tare da danginta. An kuma haɗa da wasu mambobin iyali guda takwas a yayin sacewar.
Bashir ya bayyana cewa tun bayan faruwar lamarin, masu garkuwan basu tuntuɓe su ba, lamarin da ya ƙara tayar musu da hankali. Ya ce, “Matata da ‘ya’ya mata guda biyu sun bar Abuja a ranar Alhamis zuwa Kaduna. Amma an sace su a gidan iyalinta a daren Alhamis.
“Abokaina ma’aikatan jarida, don Allah ina bukatar addu’arku. An sace ‘ya’ya mata na biyu da mahaifiyarsu, har da wasu mutane takwas a ranar Alhamis da daddare a Kaduna, inda suka je yin hutu,” inji Bashir yayin da yake bayyana da abokan aikin sa ta WhatsApp.
Leadership Hausa