Kamfanin Sadarwa na MTN Ya baiwa Gwamnatin Najeriya gudummuwar naira Biliyan Daya domin sanyawa cikin asusun tallafawa jama’a da abinci.
Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin Shugaban kamfanin Charles Ndukwe da tawagarsa a ofishinsa.
Kamfanin Sadarwa na MTN ya kuma ba da na’urorin sadarwa dubu huɗu da dari shidda domin rabawa makarantu a sassan kasar.
Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima ya sha alwashin aiki da guddummuwar ta hanyar da ta kamata.