Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin Tinubu Zata Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kano

Gwamnatin Tinubu Zata Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kano

Gwamnatin Tarayya ta lashi takobin kammala aikin hanyar da ta tashi daga Abuja Zuwa Kano.

Ministan Ayyuka David Umahi ne ya bada tabbacin hakan a yayin wani zama da ya yi da Kamfanin Julius Berger wanda su ne ke gudanar da wannan aiki.

Kamar yadda Ministan ya bayyana,Gwamnatin Tarayya za ta riƙa biyan kamfanin Julius Berger Naira biliyan 20 duk wata, domin kammala aikin gyaran titin na Abuja zuwa Kano.

David Umahi, ya kara da cewa, jumullar kudin kammala aikin su ne Biliyan 280 kuma za’a biya su na tsawon watanni 14 domin kamfanin ya kammala aikin kilomita 82 na ɓangaren ya rage a titin.

Ministan ya sanar da biyan wannan Naira biliyan 280 ne a yayin da yake kokawa kan ƙarancin kuɗaɗen gudanar da ayyukan hanyoyin.

A cewar shi, Gwamnatin Tinubu ta gaji wannan aiki ne daga Gwamnatin da ta gabata.

A baya dai al’umma sun sha kiraye-kiraye ga Gwamnatin Tarayya akan ta tabbatar da kammala wannan aiki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments