Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin Tarayya Ta Baiwa Yobe Tallafin Buhunan Hatsi 90,000 A Cikin Watanni...

Gwamnatin Tarayya Ta Baiwa Yobe Tallafin Buhunan Hatsi 90,000 A Cikin Watanni 7 – Shugaban SEMA

Daga, Muhammad Sani Chinade, Damaturu

Gwamnatin Yobe a ranar Litinin ta ce ta samu tallafin buhunan hatsi sama da 90,000 daga Gwamnatin Tarayya tun daga watan Maris din 2023.

Sakataren zartarwa na Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), Dr Muhammed Goje, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Damaturu.

Ya ce tallafin na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta a jihar.

Goje ya lissafa kayan abinci da suka hada da: buhunan shinkafa 30,000 sai dawa da masara buhuna 60,000.

Sakataren zartaswar ya yabawa gwamnatin tarayya bisa yadda take ci gaba da tallafawa kokarin gwamnatin jihar na kawar da fatara.

“Gwamnatin jihar ta yi namijin kokari wajen bayar da tallafi ga ‘yan Jihar kuma tallafin da gwamnatin tarayya ta bayar wani abin farin ciki ne ga wannan kokarin,” inji shi.

Goje ya ce tun daga lokacin ne aka raba hatsin ga marasa galihu da ke fadin kananan hukumomi 17 na jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments