An kashe wani mai zanga-zanga a Suleja a Jihar Neja, bayan wasu ɓata gari sun kwace zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi wa laƙabi da #EndBadGovernance da ake yi a fadin kasar.
Zanga-zangar, wadda ta fara da mutum 25, ta rikiɗe zuwa tashin hankali bayan wasu ‘yan daba da aka fi sani da “Yangogoni” (Masu bin bola) sun tayar da hargitsi.
Marigayin ya mutu sakamakon raunukan da ya samu yayin rikicin.
Har yanzu ba a gano ainihin dalilin mutuwarsa ba a lokacin wannan rahoton.
Ana sa ran samun ƙarin bayani yayin da lamarin ke ci gaba da gudana.
Leadership Hausa