Daga, Sani Saleh Chinade, Damaturu
Ofishin mai ba gwamnan jihar Yobe shawara na musamman kan harkokin tsaro Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam, ya gargadi al’umma musamman masu fasa karafa da aka fi sani da Baban Bola, da su guji shigowa Jihar ta Yobe da tarkace da sauran karafa da aka yi watsi da su daga wasu wurare zuwa cikin jihar.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mai bada shawarar (SA) na cewa, “wannan gargadin ya zama dole ne biyo bayan tarwatsewar wasu bama-bamai da aka yi watsi da su da wasu ‘yan ta’addan da suka tsallako daga cikin dajin Sambisa tun a baya suka ajiye a yankin Goniri yadda suka raunata biyar daga cikinsu.”
Don haka ana shawartar jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ake tuhuma ko motsin Wasu mutanen da ba’a yarda da su ba a cikin al’ummominsu.
Sanarwar ta kara da cewar sashen kawar da bama-bamai na soji na aiki ba dare ba rana don kwashe wasu na’urori da watakila an yi watsi da su a shekarun baya.