Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiAn Hallaka Shugaban Hamas, Ismail Haniyeh A Tehran

An Hallaka Shugaban Hamas, Ismail Haniyeh A Tehran

Kungiyar Hamas ta ce an kashe shugabanta, Ismail Haniyeh a birnin Tehran na Iran.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an kashe Haniyeh ne a gidansa da ke Tehran, a ziyarar da ya kai domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.

Kungiyar Falasdinawan mai rike da iko a Gaza ta ce Isra’ila ce ta kashe shugaban nata, m yayin da yake halartar rantsar da sabon shugaban Iran.

Kungiyar Hamas ta bayyana kisan a matsayin babban laifi wanda martaninsa ba zai zo da dadi ba.

Ta kuma ce Isra’ilan ta kashe daya daga cikin masu tsaron lafiyar Haniyeh, a lokacin samamen da ta kai.

Hamas ta kuma yi ta’aziyya ga Falasdinawa da Larabawa da kuma Musulman duniya da kuma a kan rashin jagoran nata.

Mafi yawan shugabannin kungiyar Hamas dai ba su fitowa fili su bayyana kansu, yayin da a gefe guda kuma, duk wadanda suka bayyana kansun to za su gama rayuwarsu ne suna wasan boyo da Isra’ila, mai neman rayuwarsu ruwa a jallo.

Kafin wannan lokaci dai ana dai ganin Ismail Haniyeh a matsayin babban jagoran kungiyar Hamas, kuma yana cikin kungiyar tun daga shekarar 1980.

Ya taba zama Firaiministan Falasdinawa a 2006, amma daga baya aka sauke shi bayan Hamas ta kwace mulkin Zirin Gaza daga hannun jam’iyyar Fatah.

A 2017 aka zabe shi shugaban bangaren siyasa na kungiyar kuma bayan shekara daya Amurka ta sanya sunansa a cikin ‘yan ta’addan da ta ke nema ruwa a jallo.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments