Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiBoko Haram Na Shirin Kutsawa Cikin Zanga-Zangar Kasar Baki Daya.in ji DSP...

Boko Haram Na Shirin Kutsawa Cikin Zanga-Zangar Kasar Baki Daya.in ji DSP Dungus

Daga, Muhammad Sani Chinade, Damaturu

Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta ce ‘yan ta’addan Boko Haram sun kammala shirin kutsawa cikin zanga-zangar da aka shirya za a fara ranar 1 ga watan Agusta a jihar Yobe da ma.kasa Baki Daya.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta fitar, wadda ta rarraba ga manema labarai a garin Damaturu.

DSP Dungus Abdulkarim, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Yobe a cikin sanarwar ya ce, bayanan sirri sun nuna cewa wasu daga kasashen waje an dauko su haya tare da hada kai da su  wajen lalata rayuka da dukiyoyi yayin zanga-zangar.

Don haka kakakin ‘yan sandan ya yi kira ga mutanen da ke shirin shiga zanga-zangar da su yi taka-tsan-tsan.

“Yayin da jihar Yobe ke murmurewa daga tashe-tashen hankula, kwamishinan ‘yan sanda, CP Garba Ahmed, ya amince da ‘yancin da tsarin mulki ya ba ‘yan kasa na yin taro cikin lumana.”

“Yayin da muke faɗakar da ’yan ƙasa game da mugun nufi da wasu ke da shi, hatta zanga-zangar lumana a wannan lokacin na iya zama wani abu dabam.”

Rundunar ‘yan Sandan ta kuma umarci masu shirya zanga-zangar da su mika sunayen su ga rundunar da kuma wuraren da za su bi yayin zanga-zangar don tantance su da kuma yadda za’a ba su kariya matukar ba su saba ka’ida ba.

“A cewar sa ayyukan ta’addancin baya-bayan nan a karamar hukumar Gujba, gami da fashewar bom (IED), sun haifar da damuwa matuka ga al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments