Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiBa Za Mu Yi Kasa A Gwiwa Ba Wajen Inganta Harkokin Tsaro...

Ba Za Mu Yi Kasa A Gwiwa Ba Wajen Inganta Harkokin Tsaro A Yobe Ba – Gwamna Buni

Daga, Muhammad Sani Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe Hon,  Mai Mala Buni ya tabbatar da cewa gwamnatin sa ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen cigaba da Inganta harkokin tsaro a fadin jihar ba.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban Darakta Janar kan harkokin ‘yan Jaridu da harkokin yada labarai  ga Gwamnnan Mamman Mohammed, ya bayyana cewa, gwamnan da ke mayar da martani kan bama-baman da aka dasa a kasuwar Buni Yadi, ya ce jami’an tsaro na cikin shirin ko-ta-kwana don cigaba da sake duba halin da ake ciki.

A cewar sa bom din da ya fashe a kasuwar shanu ta Yadin Buni an samu  rahotan  wata yarinya ta ji rauni a kafarta a wannnan lokaci.

Gwamna Buni ya umurci Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta kai daukin gaggawa ga wadanda suka ji raunuka  daukar su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar domin yi musu magani musamman ma yarinyar da tafi Jin rauni.

Ya ce jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike cikin tsanaki, ciki har da wadanda ake zargin da kuma hanyar shigarsu wannnan wuri.

Gwamna Buni ya ce ana samun ci gaba sosai a binciken da ake yi, “Ba za mu yi kasa a gwiwa ba, ba za Kuma  mu bari wani ko wasu ‘yan ta’addan kungiya su mayar da ci gaban da aka samu a harkar tsaro a jiharmu baya ba.”

Ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu taka-tsan-tsan tare da kai rahoton duk wani mutum ko jinsu wasu mutanen da ake zargi da wasu abubuwan ki ba a yankunansu, wadda ta yin hakan ne za mu kai ga nasarar kawar da ma su muggan nufi daga cikin al’umma.

A halin da ake ciki,  daga bisani sojojin sun yi  nasarar cire wasu bama-bamai biyu da aka dasa a kasuwar wadda ba su Kai ga tashi ba tukunna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments