Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiƊalibar Chibok Mai Juna-Biyu 'Yan Boko Haram 8 Ne Aka Aura Min

Ɗalibar Chibok Mai Juna-Biyu ‘Yan Boko Haram 8 Ne Aka Aura Min

Ta bayyana yadda ake tsare ‘yan mata a sansanin Boko Haram da ke dajin Sambisa.

Ɗaya daga cikin ’yan matan Chibok da aka sace a watan Afrilun 2014, mai suna Ihyi Abdul, a Jihar Borno, ta ce an tilasta mata auren maza takwas yayin da ta ke hannun Boko Haram.

Aminiya ta ruwaito yadda Rundunar Operation Haɗin Kai ta miƙa yarinyar Chibok da aka ceto tare da wasu mutum 332 ga gwamnatin Jihar Borno.

Mutum 332, ciki har da mata 110 da yara 220, an ceto su ne a yankin Bama-Pulka yayin wani samame da dakarun soji suka kai dajin Sambisa.

Da ta ke jawabi ga manema labarai a hedikwatar Operation Haɗin Kai a Maiduguri, ta ce, “Na yi tafiyar tsawon kwanaki kafin na isa wani wajen da sojojin Najeriya suke, inda suka karɓe ni da ’ya’yana.

“Na auri maza takwas kuma na haifi yara uku. Ban yi ƙoƙarin tserewa ba a baya saboda ban shirya tserewa ba sai a yanzu.

“Ba a ajiye ‘yan matan Chibok a sansani ɗaya, kuma ban san dalilin da ya sa ake tsare wasu tsare ba. Wasu daga cikinmu sun zaɓi zama a Sambisa, yayin da wasu ba su samu damar tserewa ba.

“Game da ilimi, ba zan iya cewa komai ba a yanzu, amma ba ni da tabbacin cewar zan iya ci gaba da karatu ba.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments