Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF), ta koka da yadda rashin tsaro, talauci da jahilci ke jefa yankin Arewa a baya.
A jawabinsa na ranar Litinin a Kaduna, yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Uba Sani a gidan Sir Kashim Ibrahim, shugaban kungiyar ACF, Mamman Mike Usman ya bukaci shugabanni da al’ummar yankin da su gaggauta sauya tunani da tsare-tsare marasa kyau ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban ACF ya ce: “A cikin kokarinmu, da shugabannin Arewa, da suka hada da gwamnonin jihohi, sarakuna, da sauran dattawa, sun yanke shawarar kafa ACF a shekarar 2000. Saboda bada shawarwari ta yadda za a kawar da irin wannan matsalar ta tsaro da rigingimu a yankin.
“Manufar ita ce, a hada kai a zama daya wajen wakiltar al’ummomin Arewacin Nijeriya ba tare da la’akari da siyasa, kabilanci, ko addini ba.
ACF ita ce ta yi aiki a matsayin Majalisar Jama’a ko Dattawa wacce ta buɗe idanu da kunnuwa don yin la’akari da al’amura da ci gaban da ka iya haifar da rashin jituwa, ko rikici a fadin Arewa da bunkasa ci gaban yankin
“A yau, duk da jajircewar da muka yi, samun zaman lafiya da hadin kai da ci gaba a Arewa, lamari ne da dole sai an jajirce wajen kokarin gudanar shi. Duk alkaluman da ke nuna koma baya a ci gaban bil’adama – talauci, jahilci, da rashin tsaro na rayuka da dukiyoyi – sun jefa Arewa a cikin rami mai zurfi, lallai akwai babban aiki da ke jiran duk ’yan Arewa.”
A cewarsa, ACF ta himmatu wajen bayyanawa da kare muradun al’ummar Arewa ta hanyar ayyukansu daban-daban.
Leadership Hausa