Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiAn Kafa Kwamitin Binciken Cin Zarafi Da Aikace-aikacen Hukumar Hisbah A Katsina

An Kafa Kwamitin Binciken Cin Zarafi Da Aikace-aikacen Hukumar Hisbah A Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da kwamitin da zai binciki wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta kan zargin cin zarafin mutane da Hukumar Hisbah ta yi, gami da bincike kan dukkanin aikace-aikacen Hukumar.

Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Barista Abdullahi Garba Faskari ne ya ƙaddamar da kwamitin a madadin muƙaddashin Gwamnan Jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Jobe a wani taro daya gudana a ofishin sa.

A cewar Barista Abdullahi Garba Faskari, Gwamnatin Jihar Katsina ta karɓi ƙorafi daga mutane kan zargin cin zarafi da hukumar Hisbah ta yi a wani bidiyo, inda bidiyon ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, inda aka hangi yadda ƴan Hisbah ke cin zarafin mutane a cikin sa.

Barista Abdullahi Faskari yace Gwamnati ta kafa Hukumar Hisbah domin taimakawa al’umma, haka zalika ba zata zura ido taga ana cin zarafin mutane ba.

An baiwa Kwamitin ƙa’idoji da dokoki da zai bi domin gudanar da aikin da ya ƙunshi, bincike kan gaskiyar bidiyon da ya yi yawo a kafafen sada zumunta kan zargin cin zarafin mutane da jami’an Hisbah suka yi.

Akwai kuma batun bincike kan zargin wulaƙanta mutane da jami’an Hisbah ke gudanarwa, tare da bincike kan dokar da ta kafa Hukumar Hisbah tare da gano abubuwan da suka haddasa karya dokokin da suka kaiga cin zarafin ƴan adam, gami da bayar da shawarwari kan yadda za’a magance abubuwan da aka gano.

Haka zalika, an baiwa Kwamitin aikin gano jami’an da suka ci zarafin al’umma tare da bayar da shawarwari kan yadda za’a hukunta su.

Kwamitin an kuma bashi kwanaki 10 daga ranar da aka ƙaddamar da shi domin bayar da rahoton abinda suka gano.

Daga cikin waɗanda aka ƙaddamar, akwai Kwamishinan Wasanni da Cigaban Matasa Hon. Aliyu Lawal Zakari a matsayin shugaban kwamitin, da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Addinai a matsayin mamban kwamitin, da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Shari’a a matsayin mamba.

Sauran sun haɗa da Babban Sakataren Ma’aikatar samar da tsaro da harkokin cikin gida a matsayin mamba da kuma Babban Sakataren Ma’aikatar kula da maido da yadda aikin Gwamnati ya ke a matsayin mamba, sai Shugaban Ƙungiyar Gamayyar Kungiyoyin Fararen Hula Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya a matsayin mamba, tare da Daraktan Samar da tsaro a ofishin Gwamna a matsayin mamba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments