….Muna yunkurin samar da hasken sola da bai zarce kauyuka 500 ba a karkara-Kwamishinan
Daga Rabiu Sanusi
Kwamishinan inganta harkokin karkara na jihar Kano Alhaji Abbas Sani Abbas ya bukaci al’ummar dasu sa ido wajen kula da ayukan da gwamnatin Abba Kabir Yusuf take gudanarwa da moriyar Al’umma dake Jihar.
Alhaji Abbas Sani Abbas ya bayyana hakan ne a wata zantawa da yayi da wakilan gidajen labarai na fadar gwamnatin Kano a ranar talatar nan.
Kwamishinan yace zuwan sa wannan ma’aikata akwai abubuwa masu tarin yawa, wanda ya fara da duba yanayin hanyoyin da zasu sada mazauna karkara da samun cigaba a fadin jiha.
A.S.A yace da sahilewar mai girma gwamna an samar masu da kudin da zasu gabatar da gudanar da ayuka.
“Daga nan mun kara tashi tsaye zuwa ma’aikatar Kudi ta jiha dan a samu a sakar mana kudin da mai girma gwamna ya sahile mana dan fara ayukan da yakamata.
Kwamishinan yace yazuwa yanzu sun saki shirye shiryen gudanar da ayuka guda (8) guda biyar (5)
hanyoyi sai wasu ayukan guda 3 dan bunkasa ayukan cigaba.
Haka zalika yace akwai wasu tituna guda 10 a kananan hukumomi na cikin gari dan samun yadda za’a cigaba, sai ayukan gayya dan yashe magudanan ruwa na kananan hukumomi 8 na cikin gari dan kaucewa ambaliyar ruwa.
“haka kuma akwai hanyoyi guda(3)da masu hasashen yanayi dan kaucewa wannan ambaliyar ruwa dan haka da mun kammala wannan na kananan hukumomi (8) din nan na cikin gari.
Ya kuma jaddada shirin ma’aikatar sa na shirin samar da taransfoma dan inganta wutar lantarki a kowane lungu da sako na jihar Kano da zata kai kimanin guda (500)
Kwamishinan na raya karkara yace akwai yunkurin samar da hany kilomiters guda dari biyar(500) sai rijiyoyi guda dubu biyar (5000) tare da maganar solar dan gidajen karkara da basu wuce guda 500 ba da a haska guraren da al’ummar su dan inganta rayuwar al’umma.
Abbas sani Abbas ya kuma bukaci al’ummar jihar kano da su kula da dukkan abinda za’a sama masu na cigaban da zasu fuskanta dan kaucewa batawa da kuma tabbatar karkon su