Daga, Muhammad Sani Chinade, Damaturu
A yau Asabar ne ake sa ran shugaban kasar Najeriya Ahmad Bola Tinubu zai kawo ziyara Jihar Yobe don Bude Wasu muhimman ayyukan raya kasa da gwamnatin Jihar karkashin Gwamna Mai Mal Buni ta gudanar
Da ya ke jawabi ga manema labarai a babban dakin taro na kungiyar ‘yan Jaridu ta Jihar (NUJ) da ke garin Damaturu, kwamishinan cikin harkokin gida, yada labarai da al’adu na Jihar Alhaji Abdullahi Bego ya ce dukkan shirye-shirye sun kammala don karbar mai girma shugaban kasar a yau Asabar.
A cewar sa shugaban kasar zai bude bada tallafin kayan aikin gona na bilyoyin Nairori ga manoman Jihar da gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta tanadarwa manoman Jihar da ya ke akasarin al’ummar Jihar ta Yobe manoma ne.
Don haka ya bada tabbacin gwamnatin Jihar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa a jihar da Kuma cigaba da Bada taimako ga harkokin na noma da Sauran bangarorin raya kasa ga al’ummar Jihar ta Yobe.