Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiKishin Ƙasa Nasa Agaba Fiye Da Tara Riba – Dangote

Kishin Ƙasa Nasa Agaba Fiye Da Tara Riba – Dangote

Hamshaƙin attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya fi fifita kishin ƙasa a kan samun riba kawai cikin harkokinsa na kasuwanci inda hakan ya sa ya fi mayar da hankali a kan kafa kamfanoni a Nijeriya har ma da Afirka baki xaya domin nahiyar ta zama mai dogaro da kanta.

Attajirin wanda yake bayani ga manyan shugabannin kafafen yaɗa labarai da ya karɓi baƙuncinsu a sabuwar matatarsa ta mai da ke yankin Lekki na Legas, ya ƙara da cewa, matuqar qasashenmu na Afirka ba su mayar da hankali a kan samar da kamfanonin da za su riƙa sarrafa abubuwa na buƙatun al’ummominsu a cikin gida ba, tabbas, za su ci gaba da fitar da ayyukan  yi zuwa kasashen duniya, su kuma suna caka wa kansu wuka ta hanyar shigo da karin talauci cikin kasashensu.

Kamar yadda ya yi bayani, daga irin wannan kishin ne, ya samar da matatar mai da za ta rika tace danyen mai ganga 650,000 a kullum da zai wadaci Nijeriya da kuma fitarwa zuwa kasashen waje.

Ya ba da tabbacin cewa a karshen wannan watan da muke ciki, man fetur da matatarsa take tacewa zai shiga kasuwa a Nijeriya.

“Ka san wahalar fetur ana yin ta idan ka duba tarihi tun lokacin Gowon, a 1972, ba a samun mai ya wadata.

To amma idan Allah ya yarda, idan muka soma (fitar da mai), Nijeriya ba za ta iya shan fiye da rabin abin da za mu yi ba… In sha Allahu daga wannan watan (Yuli) za mu soma (fitarwa).”

A cewar Dangote lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP Hausa.

Dangote wanda kamfanoninsa ke zaman rukuni daya tilo mafi samar da ayyukan yi a Nijeriya mai ma’aikata fiye da 100,000, ya bayyana cewa ya himmatu wajen ganin an bukasa harkokin noma a Nijeriya inda yanzu haka ya mayar da hankali a kan noman shinkafa, da rake da kuma tumatir tare da kakkafa masana’antun sarrafa su.

“Mun samar da kamfanin sarrafa tumatir a Kano, za mu bai wa manoma kudi su yi noma kuma ba tare da fargabar rashin samun kasuwar sayar da amfanin gonarsu ba, mu za mu saya, kuma idan sun ga farashin da za mu saya ya yi kadan, za su iya kaiwa inda suke so su sayar… a Nijeriya, kasarmu ta noma da ake nomawa ba ta fi kashi 8 cikin 100 kacal ba.” Ya bayyana.

Bugu da kari, Alhaji Dangote ya nunar da cewa, kamfaninsa na taki ya dakatar da sayarwa a kasashen waje saboda yadda ake bukatar takin a gida a halin yanzu.

“A kamfanin takinmu muna da taki na Urea wanda ba samfurin NPK ba, da ya fi karfin abin da Nijeriya ke nema.

Kashi 20 cikin 100 ne kawai Nijeriya za ta iya dauka, amma ragowar na kaiwa kasar waje ne mu sayar.

Amma kowane irin taki ne in dai Urea ne ake nema muna da shi kuma muna sayarwa, amma a yanzu haka ma ba ma fitarwa waje duka muna sayarwa a cikin gida saboda yanzu (damina) lokacin neman taki ne… Idan muna da gas, za mu iya yin takin har tan miliyan uku, to amma gaba dayan kasuwar nan (Nijeriya) ba ta ma kai tan miliyan daya ba na Urea.” In ji shi.

Har ila yau, zauren tattaunawar Attajirin da shugabannin kafafen yada labarai ya dau jinjina yayin da aka ji yana bayyana cewa ba shi da gida a Amurka ko Landan, sannan hatta gidan da yake sauka a Abuja na haya ne ba na kashin kansa ba.

Ya ce sha’awarsa ga ci gaban masana’antu a Nijeriya shi ne kadai dalilin da ya sa ya yanke shawarar kin mallakar gidaje a kasashen waje.

Dangote ya bayyana cewa ya taba samun gida a Landan, amma ya sayar da shi a shekarar 1996.

“Ba ni da gida a Landan ko Amurka saboda ina so in mayar da hankali kan bunkasa masana’antu a Nijeriya. Na dauka cewa idan ina da wadannan gidajen, ana iya samun wani dalili da zai dauke hankalina zuwa zama a can.

“Ina matukar sha’awar ganin ci gaban Nijeriya kuma ban da gidana na Legas, ina da wani a jihata ta asali Kano da kuma na haya a Abuja.” In ji shi.

A jawabinta na rufewa, Babbar Daraktar Harkokin Kasuwanci na Kamfanonin Dangote, Fatima Dangote, ta yaba wa mahaifin nasu a kan yadda yake nuna kishin kasa karara cikin harkokinsa na kasuwanci.

Ta kara da cewa, “Ban taba ganin wanda ya kai mahaifina aiki tukuru ba, wani lokaci ina mamakin yadda ba ya jin kasala a jikinsa.

Sannan duk kamfanin da zai kafa abin da yake fara dubawa shi ne kishin kasa ba riba ba, domin akwai abubuwan da zai iya yi da yawa kamar zuba kudi a kamfanoni irin na su Elon Musk ko na Microsoft da zai samu riba mai yawa, amma bai yi hakan ba, yana duba kishin ci gaban kasa ne da nahiyarmu.

Da ma a ce mun sami karin jajirtattun mutane kamar mahaifina a Nijeriya, kasar za ta fi samun ci gaba.” Ta bayyana.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments