Daga Muhammad Sani Chinade, Damaturu
A ci gaba da aikin da ta ke Yi na yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram/ I SWAP rundunar Operation Lake Sanity 2, rundunar hadin gwiwa ta (MNJTF) ta kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 9 tare da kwato manyan makamai da alburusai a ranakun 17 da 18 ga watan Yulin 2024.
A ranar 18 ga Yuli, 2024, sojoji sun kai wani samame a kauyen Yashinti, karamar hukumar Nganzai jihar Bornon Najeriya a yayin musayar wuta, an kashe ‘yan ta’adda 4. Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindiga kirar AK-47 guda daya, da akwatunan albarusan AK-47 guda 3, da harsashi na musamman nau’in 7.62mm x 39mm.
A wani aikin share fage na daban a yankunan garuwan Gajiram, Marram, Tumtumari, Layinma, Kulunkiya, Gadayi Tumtumari, da Kodayi a karamar hukumar Nganzai, sojojin sun kashe wasu Karin ‘yan ta’adda 4 da suke yunkurin kawo cikas ga ayyukan noma.
Wani yaro dan shekara 10 mai suna Mustapha Bukar da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da shi, an kubutar da shi tare da hada shi da iyalansa wadda a wannnan samame Sojojin sun kwato makaman da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda 2, da akwatunan albarusai 4, da alburusai 30 na nau’in 7.62mm da 30mm.
Bugu da kari, dakarun na rundunar MNJTF sun kai wani harin kwantan bauna da dare a wata matattarar ‘yan ta’adda da aka gano a karamar hukumar Kukawa wadda aka kashe ‘yan ta’adda guda a wannan farmakin. Sojojin sun kwato bindiga kirar AK-47 daya, da harsashi 118 nau’in 7.62mm.
Wadannan ayyuka sun nuna yadda rundunar hadin gwiwar MNJTF ke ci gaba da kokarin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tafkin Chadi.
Haka nan nasarar da suke samu wajen kawar da ‘yan ta’adda da kwato makamai ba kawai yana raunana karfin ayyukan ‘yan tada kayar baya ba ne, har ma da samar da kwanciyar hankali da aminci ga al’ummar yankin