Daga Rabiu Sanusi
An jaddada yunkurin gwamna Abba Kabir Yusuf na kokarin kawo chanjin bai daya a bangaren noma a fadin jiha Kano baki daya
Wannan na zuwa ne daga bakin shugaban riko na karamar hukumar Gwale Hon Abubakar Mu’azu Moja a wata zantawa da manema labarai yayin da tawagar sa suke adana takin da sauran Kansilolin sa baki daya.
Hon Abubakar Mojo yace a yadda mai girma Gwamna Abba Kabir ya maida hankali wajen chanza akalar jihar ta hanyoyi daban-daban na cigaban jama’ar sa.
Hon Mojo ya kuma bayyana cewa shima a karamar hukumar Gwale yayi shi mai girman gaske na kawo chanji na cigaba da zasu tallafawa jama’ar sa da ta fuska mabanbanta.
“Sakamakon bukatar taimakon karamar hukumar Gwale ya sa muka tashi tsaye tare da fita dan samo hanyoyin da zasu bamu damar tallafama mutanen mu dan basu damar tsayawa da kafafu baki daya.”
Kantoman rikon ya jaddada cewa ya zuwa yanzu dai sunyi shiri na musamman dan ganin yadda mai girma Gwamna yabasu wannan amana sun isar da ita yadda yakamata.
“Yadda kuke gani yanzu haka akwai wannan taki da gwamnati ta amince mana mu raba ga al’umma asalin manoman karamar hukumar Gwale dan haka zamu bada kamar yadda aka umarce mu.”
Abubakar Mojo ya tabbatar ma da al’ummar wannan jiha cewa shidai ya dade baiga an bada takin noma ga manoba kai tsaye daga tushe tun lokacin Jagora Dr Rabiu Musa Kwankwaso sai awannan karo na Magajin sa.
“Bayan wannan dama da aka bada na tallafin taki, haka zalika akwai batun ayukan da zamu gabatar irin na gyaran magudanan Ruwa da samama matasa hanyoyin dogaro da kai.
Kantoman ya kuma bukaci jama’ar jiha dasu kara dagewa wajen cigaba da yima Gwamna Abba Kabir addu’a da jihar baki daya.