Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiSojoji Sun Damke Mutane 7 Tare Da Kwato Makamai A Filato

Sojoji Sun Damke Mutane 7 Tare Da Kwato Makamai A Filato

Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ta rundunar sojojin Nijeriya ta III da ke Rukuba kusa da Jos, sun kama wasu mutane 7 tare da kwato makamai da alburusai iri-iri daga hannun al’ummar yankin Fann da ke karamar hukumar Barkin-Ladi a jihar Filato.

Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar Sojan kasa na sashin, Maj. Aliyu Danja ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.

Danja ya ce, kamen tare da kwato makaman ya biyo bayan wani samame da sojoji suka kai tsakanin 16 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan Yuli.

Maj. Danja ya ce, makaman da aka kwato a yayin samamen sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda shida, bindigogin AK-47 na gida guda 16, bindigu kanana 15, da sauran harsashe.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments