Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeTsaroGwamna Buni Ya Umarci Jami’an Tsaro Da Su Kamo Masu Safara Da...

Gwamna Buni Ya Umarci Jami’an Tsaro Da Su Kamo Masu Safara Da Ta’ammali Da  Miyagun kwayoyi 

Daga, Muhammad Sani  Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni,  ya umarci jami’an tsaro a jihar da su damke mutane ko kungiyoyin da ke da hannu wajen safara da ta’ammali da miyagun Kwayoyin sa maye da dangogin su da aka haramta ta’ammali da su cikin al’umma.

Gwamnan ya ba da umarnin ne a ranar Laraba a  yayin kaddamar da yakin neman sake fasalin da’a (Operation Gyaran Hali) a hukumance a jihar.

Gangamin wanda ma’aikatar kula da harkokin addini da da’a ta jihar Yobe (MORAER) ta shirya da nufin kawo sauyi mai kyau a cikin al’umma.

Buni ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta tallafa wa jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen yakar wannan mummunar annoba ta shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar su.

Don haka ya yi kira ga shugabannin hukumomin tsaro da su shiga a dama da su wajen  tabbatar da an tsaftace  gidaje don tabbatar da cewa, babu wasu daidaikun mutanen da za su iya zagon Kasa ga wannan gagarumin shiri na yaki da miyagun kwayoyi.

Ya ce, hakika kaddamar da shirin na farfado da da’a ya zo a kan lokaci, duba da yadda gurbacewar tarbiyya ta yi tsamari  a cikin al’umma, musamman a tsakanin matasan mu.

Gwamna Buni ya bayyana cewa, a al’adance tun zamanin tsohuwar Daular Kanem Bornu da kuma tasirin Musulunci, al’ummomi sun shahara wajen gaskiya da rikon amana da sauran su, amma abin bakin ciki a cewarsa wadannan kyawawan halaye na ci gaba da tabarbarewa a wannnan lokaci.

A cewar Buni, karuwar shan haramtattun abubuwa, musamman ma kwayoyi na da matukar tayar da hankali, kuma ya yi kira da a dauki matakin gaggawa da dabarun dakile bala’in da ake samu don ceto al’ummomi jiha da kasa baki daya daga fadawa cikin mummunan yanayi musamman ga matasa manyan gobe.

“Saboda haka ya zama wajibi ga duk masu ruwa da tsaki da suka hada da gwamnati da sarakunan gargajiya da malaman addini da iyaye da masu iyaye da su hada kai da jami’an tsaro wajen yaki da miyagun kwayoyi a jihar da ma kasa baki daya

“Yawancin laifuffuka da ke faruwa cikin al’umma suna da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi, don haka ya kamata al’umma su fallasa duk Masu aikata wannnan mummunan halayya da ke  yankunansu da suka shafi miyagun ƙwayoyi maimakon maimakon boye su, ta yin haka ne zai sa a samu matasa masu hankali da hazaka.”

“Don haka a  matsayin su na masu kula da al’adu da kyawawan dabi’u, ana ba da umarni ga cibiyoyin gargajiya da su karfafa shirye-shiryen wayar da kan jama’a, da kuma sabunta yakin da gwamnati ke yi da laifukan da suka shafi muggan kwayoyi,” in ji Gwamna Buni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments