Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiMahaifiyar Rarara Ta Shaki Iskar 'Yanci Daga Hannun ‘Yan Bindiga 

Mahaifiyar Rarara Ta Shaki Iskar ‘Yanci Daga Hannun ‘Yan Bindiga 

Mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar nan na Arewacin Nijeriya, Dauda Kahutu Rarara ta kubuta daga hannun ‘yan bindigar da suka sace ta.

Idan ba a manta ba an sace mahaifiyar mawakin, Hauwa’u Adamu a ranar 28 ga watan Yuni, 2024 a kauyen Kahutu da ke karamar hukumar Danja a Jihar Katsina.

Sai dai bayan sace tsohuwar mai shekaru 75 a duniya, jami’an ‘yansanda a jihar suka baza koma, inda suka cafke mutum biyu da suke zargi da hannu a sace ta.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce an sace mahaifiyar mawakin da misalin karfe 1:30 na dare.

Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da kubutar mahaifiyar mawakin, amma babu cikakken bayani ko an biya kudin fansa kafin sakinta.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments