Daga, Muhammad Sani Chinade, Maiduguri
Gwamnatin jihar Borno ta kudurta daukar nauyin daliban Jihar da ke son yin karatun Sinanci a kasar Sin.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin babban Sakataren Hukumar ba da tallafin karatu ta Jihar Borno, Bala Isa a wata hira da manema labarai a Maiduguri.
Bala ya ce baya ga harshen Sinanci, Gwamna Babagana Zulum ya kuma amince da bayar da tallafin karatu na farko a fannin likitanci, (MBBS) da Injiniya a manyan cibiyoyi a kasar Sin ga daliban Jihar da suka cika sharuddan da ya dace kan takardun su na kammala jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC).
A cewarsa, masu neman karatu akan harshen na Sinanci dole ne su sami sakamako mai kyau a fannin fasaha, yayin da su kuma masu neman kwarewa akan harkokin aikin likitanci da injiniya dole ne su samu sakamako mai kyau akan harshen Turanci, Lissafi, da Wasu bangarorin kimiyya da suka hada da Biology, Chemistry da Physics.
“A cewarsa ya kamata daliban su sami mafi karancin kashi 75 na sakamako mai kyau a jarrabawar takardar shaidar Afirka ta Yamma (WAEC) akan karatun likitanci (MBBS)da kashi 65 a WAEC akan karatun Injiniya, wadda duk Mai bukata ya yi kokari neman yin hakan kafin ranar 15 ga watan gobe na Augusta ta hanyar shiga adireshin da gwamnatin ta samar na yanar gizo musamman ga daliban da ke tsakanin shekara 18 zuwa 25 na haifuwa.” In ji Bala Isa.