Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiKu Bai Wa Mabukata Shinkafar Da Aka Ba Ku – Gwamnatin Tarayya...

Ku Bai Wa Mabukata Shinkafar Da Aka Ba Ku – Gwamnatin Tarayya Ga Gwamnoni 

Gwamnatin Tarayya ta ce ta bai wa kowace jiha daga cikin jihohi 36 na Nijeriya da kuma babban birnin tarayya Abuja, tirelar shinkafa 20 domin raba wa talakawa.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne, ya bayyana hakan bayan kammala taron majalisar zartarwa (FEC), na ranar Litinin.

Ya ce kowace tirela tana dauke da buhun shinkafa 1,200 mai nauyin kilogiram 25 kuma an mika su ga gwamnonin jihohi a yunkurin rage radadin da talakawa suke ciki na karancin abinci da tsadar rayuwa.

Gwamnatin Tarayya ta ce tana fatan gwamnonin jihohin za su raba kayan abincin ga mabukata a matakin jiha da kananan hukumomi.

Ana dai fama da tsadar kayan abinci da ake alakantawa da matsalolin tattalin arziki wanda janye tallafin mai da matsalar tsaro suka haddasa.

A gefe guda kuma, ana tunanin gwamnatin ta yi haka ne domin tausar zukatan wasu matasan Nijeriya da ke shirye-shiryen tsunduma zanga-zanga kan matsin rayuwa.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments