Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Yusuf Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Samar Da Masarautu Uku Masu...

Gwamna Yusuf Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Samar Da Masarautu Uku Masu Daraja Ta Biyu A Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautu ta jihar Kano ta shekarar 2024, wacce ta kafa sabbin masarautu guda uku a jihar.

Gwamnan, yayin da yake godewa majalisar dokokin jihar kan yadda ta saurari bukatun jama’a, ya kuma yaba da yadda ‘yan majalisar dokokin jihar suka jajirce wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu.

Sabbin masarautun guda uku sun hada da masarautar Gaya da ta kunshi kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu; Masarautar Rano ta kunshi kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, sai kuma masarautar Karaye, wadda ta kunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo na jihar.

Shugaban Majalisar, Jibril Falgore ne ya mika wa Gwamnan Jihar kudirin dokar a fadar gwamnati da ke gidan Gwamnatin Jihar.

Shugaban majalisar ya godewa gwamnan jihar bisa bai wa majalisar jihar hadin kai tare da yin alkawarin ci gaba da yin hadin gwiwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments