Sunday, April 27, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeWasanniMessi Ya Bar Tarihi A Ƙwallon Ƙafa Bayan Lashe Kofin Copa America

Messi Ya Bar Tarihi A Ƙwallon Ƙafa Bayan Lashe Kofin Copa America

Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa wanda ke buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami kuma tsohon ɗan ƙwallon FC Barcelona Lionel Andre Messi ya sake karya wani tarihi a Duniyar ƙwallon ƙafa bayan ya lashe kofin Copa America da aka kammala a katsar Amurka.

Da wannan ne Messi mai shekaru 38 ya lashe kofuna 45 jimilla a tarihin kwallon kafa da ya shafe shekaru 20 yana yi,wanda kuma hakan yasa ya zama ɗan wasan da yafi lashe yawan kofuna a tarihi.

Messi wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na Balloon d’or sau 8 jimilla,ya jagoranci ƙasar Ajantina domin lashe wannan kofi na bana wanda kuma shi ne na 3 da ƙasar ta lashe a ƙasa da shekaru huɗu.

Yanzu Messi ya karya tarihin da tsohon abokin wasansa a FC Barcelona Dani Alves ya kafa na dan wasan da yafi lashe kofuna a tarihin ƙwallon ƙafa.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments