Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiTinubu Ya Taya Sheikh Dahiru Bauchi Murnar Cika Shekaru 100

Tinubu Ya Taya Sheikh Dahiru Bauchi Murnar Cika Shekaru 100

Shugaba Bola Tinubu ya taya fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi murnar cika shekaru 100 a duniya.

Tinubu, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya sanar a ranar Talata, ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin mutum mai girma wanda ya bayar da gudummawa sosai ga addinin Musulunci.

Ya gode wa shugaban Tijjaniyyar bisa sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi da kuma kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya.

“A wannan muhimmin lokaci, shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Sheikh koshin lafiya da daraja,” in ji Ngelale.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments